Sakataren Gwamnatin Jiha a Najeriya Ya Rasu bayan Ya Gamu da Hatsarin Mota
- Sakataren Gwamnatin jihar Ondo, Temitayo Oluwatuyi Oluseye ya yi bankwana da duniya bayan fama da raunin haɗarin mota
- An nada Oluseye a matsayin SSG a ranar 24 ga Janairu, 2024, kuma ya yi hidima da kwazo da jajircewa ga jiharsa har zuwa mutuwarsa
- Mutuwarsa ta girgiza al'ummar jihar Ondo da Akure, inda mutane da dama ke alhini da jimami kan rashin shugaba mai kishin jama’a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Akure, Ondo - An shiga alhini bayan sanar da rasuwar sakataren gwamnatin jihar Ondo, Temitayo Oluwatuyi Oluseye.
Marigayin ya rasu ne a yau Asabar 4 ga watan Janairun 2024 bayan gamuwa da hatsarin mota da ya afku a ranar 15 ga watan Disambar 2024.

Asali: Facebook
An fadi musabbabin mutuwar Sakataren gwamnatin jiha
The Nation ta bayyana cewa Oluseye ya mutu ne sakamakon raunin haɗarin mota da ya faru a watan Disambar 2024 inda ya dade yana jinya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Aiyedatiwa ya naɗa Oluseye a matsayin SSG a ranar 24 ga Janairu, 2024, inda ya yi aiki tukuru wajen hidimtawa jiharsa.
Duk da kokarin likitoci wajen ceton rayuwarsa, rashin lafiyarsa ta tsananta har ya ce ga garinku.
Al’ummar Akure, garinsa na asali, da sauran yan jihar suna cikin jimami kan wannan rashi na babban jagora.
Kwamishinan yada labarai a jihar, Wale Akinlosotu ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Punch a yau Asabar.
Har yanzu, gwamnatin jihar Ondo na shirin bayyana cikakkun bayanai kan shirye-shiryen jana’izarsa da kuma yadda za a girmama tarihinsa.
A matsayin mutum mai kishin aiki, an bayyana cewa tarihinsa zai ci gaba da kasancewa abin tunawa a jihar Ondo.
Kwamishinar harkokin mata a Bayelsa ta rasu
Mun ba ku labarin cewa Gwamnatin Bayelsa ta sanar da rasuwar Kwamishinar Harkokin Mata, Elizabeth Bidei, mamba a majalisar zartarwa.
Sanarwar gwamnatin jihar ta nuna alhini ga iyalan marigayiyar, musamman mijinta, Cif Jackson Bidei da 'ya'yansu.
Gwamnati ta yaba wa sadaukarwar Mrs. Bidei wajen bunkasa rayuwar mata a jihar, tana mai cewa za a ci gaba da tuna kyawawan ayyukanta.
Asali: Legit.ng