"Ba Gwamnati Ta Jawo Tsadar Rayuwa ba," Malamin Musulunci Ya Faɗawa Ƴan Najeriya Gaskiya

"Ba Gwamnati Ta Jawo Tsadar Rayuwa ba," Malamin Musulunci Ya Faɗawa Ƴan Najeriya Gaskiya

  • Babban malamin addinin Musulunci a Ibadan, Sheikh Ahmad Dhikrullah ya ce talakawa ke jawo ma kansu wahalhalun da ake ciki
  • Shehin malamin ya bayyana cewa shugabanni da talakawa kowa ya san laifin da yake aikatawa na sabon Allah, wanda su ne suka jawo wahala
  • Ya buƙaci ƴan Najeriya su daina ɗaura wa shugabannin laifin halin ƙuncin rayuwar da ake fuskanta a kasar nan

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ibadan, Oyo - Sheikh Ahmad Dhikrullah ya buƙacin 'yan Najeriya su daina zargin gwamnati kan kalubalen matsin tattalin arzikin da suke fuskanta a kasa.

Fitaccen malamin Musuluncin ya shawarci ƴan ƙasa su lalubo damarmakin da za su inganta rayuwarsu, su daina ɗora laifin komai a kan gwamnatin Najeriya.

Sheikh Ahmad Dhikrullah.
Sheikh Ahmad Dhikrullah ya ce yan Najeriya suna da laifi a halin kuncin rayuwar da ake ciki Hoto: Sheikh Ahmad Dhikrullah
Asali: Facebook

Malamin wanda ya kafa ƙungiyar Al Haqdeen International Islamic Society, ya faɗi haka ne a Ibadan yayin rufe taron Hijirah Mukhayam na 2024, Tribune ta kawo.

Kara karanta wannan

"Babu sauran sansanin ƴan bindiga a jihata," Gwamna a Arewa ya cika baki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan Najeriya ne suka jawowa kansu wahala

Sheikh Ahmad ya ce duk da ana cikin wahala da matsi a ƙasar nan, ba duka ba ne laifin gwamnati, mafi yawan matsalolin mutane ne suka jawo ma kansu.

“Ba Allah ya kawo faɗuwar tattalin arziki ko matsin rayuwa ba, domin ba a jingina mummunan abu ga Allah," in ji Malamin.

Shehin Malamin ya cw cin hanci da rashawa, aikata miyagun laifuka da saɓo sun zama ruwan dare, jami'an gwamnati da talakawa kowa na aikata lafuffuka.

Malamin ya bukaci a daina ganin laifin gwamnati

Don haka Sheikh Ahmad ya yi kira ga dukkan yan Najeriya, masu kudi da talakawa su daina saurin yanke hukunci da ɗorawa gwamnati laifi.

Ya shawarci shugabanni da talakawa su yi taka tsan-tsan da kalaman da za su fito daga harshensu da ayyukansu, su yi amfani da su ta hanyar da ta dace.

Sheikh Dhikrullah ya ce yanzu akwai ƙarancin tsoron Allah, yana mai cewa mafi yawan mutane sun fi tsoron mutane ƴan uwansu kuma sun fi girmama kuɗi.

Kara karanta wannan

"Ka fito ka faɗawa mutane gaskiya," Peter Obi ya kwancewa Tinubu zani a kasuwa

Malamin ya ƙara da cewa kalubale da wahalhalun da ake fuskanta sakamakon fushin Allah ne kuma ya shafi kowa, masu kuɗi da talakawa.

Menene mafita daga wannan halin?

Ya ce za a samu mafita daga matsalolin Najeriya ne idan mutane suka gyara halayensu suka koma ga Allah, ya ce, “Kada mu yaudari kanmu. Muna girbar abin da muka shuka ne.

“Babu mai gaskiya, kowa yana aikata saɓo, Idan ka lalata rayuwar wasu, taya kake so rayuwarka ta yi kyau kuma ta zama mai sauƙi?”

Wani magidanci, Musa Ahmad ya goyi bayan kalaman Sheikh Ahmad, ya ce tabbas wasu abubuwan ƴan Najeriya ke jawo ma kansu.

Musa ya shaidawa wakilin Legit Hausa cewa son rai da son tara abin duniya na cikin abubuwan da suka jefa al'umma cikin halin ƙunci.

"Idan ma gwamnati na da laifi to mutane sun fi laifi, yanzu fa an manta da Allah, yanzun samun mai tsoron Allah musamman kan abin duniya sai an tona.

Kara karanta wannan

Abin da Tinubu ya fadawa gwamnonin Najeriya a Lagos, ya ba su shawara

"Saɓa wa Allah ya zama ruwan dare, mutane suna ganin kamar wasu abubuwan sun zama halak, taya zamu ga daidai? Taya zamu samu shugabanni na gari?" in ji shi.

Malamin musulunci ya yi hasashen 2025

A wani rahoton, kun ji cewa wani malamin Musulunci ya hango tarin matsslolin da ka iya dabaibaye Najeriya a shekarar 2025.

Farfesa Sabit Ariyo Olagoke ya bayyana cewa za a samu rikici mai zafi tsskanin ƴan siyasa a sabuwar shekara, ya ba da shawarin matakan da ya dace a ɗauka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262