Gwamna Babagana Zulum Ya Faranta Ran Manoman Jihar Borno

Gwamna Babagana Zulum Ya Faranta Ran Manoman Jihar Borno

  • Gwamnatin Babagana Zulum na Borno za ta saidawa manoman jihar man fetur kan N600 duk lita
  • Tallafin man na Zulum zai shafi manoman da ke yankunan da ke fama da matsalar rikicin Boko Haram
  • Zulum ya zo da tsarin ne domin sauƙaƙewa manoman raɗaɗin da matsalar 'yan ta'adda ta jefa su a ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno, ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta sauke farashi man fetur ga manoman yankunan da ke fama da matsalar Boko Haram.

Zulum ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta sanya tallafin man fetur ta yadda manoman za su riƙa siyansa kan N600 duk lita ɗaya.

Gwamna Zulum zai siyarwa manoman jihar Borno man fetur kan N600 duk lita
Gwamna Babagana Zulum zai sayarwa manoman Borno fetur kan N600 duk lita
Asali: Original

Zulum zai mayarwa manoma mai N600 duk lita

Gwamnan ya bayyana hakan ne ranar Juma'a a garin Bama, yayin da yake ƙaddamar da rabon kayayyaki ga manoma 5000 da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu.

Kara karanta wannan

Ana batun tsadar mai, gwamnatin Sokoto ta samar da shirin saukaka zirga zirga

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Dailytrust ta ruwaito gwamnan yana bayyana cewa, za a riƙa saidawa manoman man da ake saidawa kan N1,000 zuwa N1,200 a cikin Maiduguri a kan N600 duk lita.

Gwamnan ya yi hakan ne domin ragewa manoman raɗaɗin da suke ciki sakamakon shekarun da suka shafe suna fama da rikice-rikicen masu tayar da ƙayar baya.

Zulum ya raba fanfunan feshi da injinan ban ruwa

Da yake zantawa da manema labarai a ranar Asabar, babban mai taimakawa gwamnan kan kafafen sadarwa na zamani Abdulrahman Bundi, ya bayyana cewa gwamnatin za ta riƙa siyo man sai ta sanya tallafinta a ciki.

Bundi ya ƙara da cewa gwamnan ya raba kayayyakin noma da suka haɗa da buhunan taki 2000, fanfunan feshin magani 1000 da kuma injinan ban ruwa guda 620 kamar yadda jaridar The Punch ta wallafa.

Haka nan ya ce Gwamna Zulum ya yi matuƙar godiya ga Gwamnatin Tarayya, kan irin gudunmawar da take ba shi a yunƙurinsa na dawo da duka mutanen zuwa muhallansu.

Kara karanta wannan

'Na san za a zage ni': Tinubu ya fadi shirin da yake yi wa Najeriya

Za a samu sauƙi

Wani mazaunin Borno mai suna Aliyu Muhammad ya yaba da matakin da gwamnan ya ɗauka na sauƙaƙa farashin fetur ga manoman.

Ya nuna cewa hakan zai taimaka musu wajen yin noman rani a sauƙaƙe domin yankin da suke ana ayyukan noma sosai kafin zuwan matsalar rashin tsaro.

"Abin yana da kyau domin akwai buƙatar a samar musu da tallafi ta yadda idan suka koma gidajensu za su rungumi harkar noman da suka saba da hannu bibbiyu."
"Za a samu sauƙi sosai kuma wannan abin da gwamna ya yi, abin a yaba ne."

- Aliyu Muhammad

Zulum ya biya basussukan 'yan fansho da giratuti

A wani labarin na daban da Legit ta wallafa, kun karanta cewa Gwamna Zulum ya biya basussukan da 'yan fansho da giratutin Borno ke bin gwamnatin jihar.

Gwamnan ya amince da ware maƙudan kuɗaɗe domin biyan basussukan 'yan fanshon na tsakanin shekarar 2019 zuwa 2021.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng