Rigima Ta Barke Tsakanin Sarki da Wazirinsa a Arewa, Lamarin Ya Kai ga Bugun Juna

Rigima Ta Barke Tsakanin Sarki da Wazirinsa a Arewa, Lamarin Ya Kai ga Bugun Juna

  • An samu matsala tsakanin Sarkin Wase, Alhaji Muhammadu Sambo Haruna, da Wazirinsa, Alhaji Muhammadu Badamasi, wanda ya kai ga rikici a fada
  • Sarkin ya zargi Waziri da rashin biyayya, wanda ya kai ga fada tsakaninsu har aka kai batun ga 'yan sanda domin bincike da daukar mataki
  • Yan sanda sun ce sun kammala bincike kuma sun kai batun kotu, amma har yanzu ba a ji ta bakin mai magana da yawun fadar ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jos, Plateau - An samu rashin jituwa da ta kunno kai a karamar hukumar Wase ta jihar Plateau tsakanin Sarki da wazirinsa.

Sarkin Wase, Alhaji Muhammadu Sambo Haruna, da Wazirinsa, Alhaji Muhammadu Badamasi sun gwabza wanda har ya kai ga yan sanda.

An gwabza tsakanin Sarki da wazirinsa a Jos
Sarki ya yi fada da wazirinsa kan zargin rashin biyayya wanda ya kai ga zuwa ofishin yan sanda a Plateau. Hoto: Legit.
Asali: Original

Sarki da Wazirinsa sun yi faɗa a fada

Kara karanta wannan

Rikici ya ƙara tsanani, an gano mai zuga gwamna ya yi wa Bola Tinubu 'rashin kunya'

Daily Trust ta ce matsalar ta samo asali ne daga wani umarni da Sarkin ya bayar wanda Waziri ya ki bi yadda ya kamata, lamarin da ya sa Sarkin ya nuna rashin jin dadi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyoyi sun tabbatar cewa a farkon makon nan, Sarkin ya yi wa Waziri tambaya kan dalilin rashin yin aikinsa, amma ya mayar masa da martani cikin zafi.

Wannan ya fusata Sarkin har ya tashi daga karagarsa ya nufi Waziri, lamarin da ya rikide zuwa rikici har da bugu.

Rahotanni sun ce Sarkin yana ganin martanin Waziri a matsayin barazana, hakan ya sa ya kai rahoton lamarin ga 'yan sanda.

Matakin da yan sanda suka dauka

A cewar yan sanda, sun yi kokarin kama Waziri a daren ranar, amma ya ce al’adar gargajiya ba ta yarda a kama shi da daddare ba, kuma ya yi alkawarin kai kansa ofishin 'yan sanda washegari.

Kara karanta wannan

Matasa sun lakadawa basarake duka kan nada limamin Juma'a, an ceto rayuwarsa

Majiyoyin 'yan sanda daga Jos sun tabbatar da cewa an gama bincike kuma an shigar da batun a gaban kotu.

Duk da haka, ba a samu damar jin ta bakin mai magana da yawun fadar ba, haka zalika jami’in hulda da jama’a na 'yan sanda, DSP Alabo Alfred, bai yi tsokaci kan lamarin ba.

An ce rigimar ta samo asali ne tun daga tsohuwar rashin jituwa tsakanin Sarkin da Waziri, wanda har yanzu ba a warware ba.

An lakada wa Basarake duka a Osun

Kun ji cewa matasa a Ido-Osun a jihar Osun sun lakada wa sabon sarki duka kan nada sabon limami da ya jagoranci sallar Juma'a.

Oba Olaiya ya zama sarki ba tare da amincewar al’ummar Ido-Osun ba, hakan ya haifar da rikici tsakanin sassan biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.