Ana Batun Korarsu, 'Yan Ta'addan Lakurawa Sun Sake Sabon Ta'addanci a Kebbi
- Ƴan ta'addan ƙungiyar Lakurawa sun kai wani harin ta'addanci a ƙaramar hujumar Argungu ta jihar Kebbi
- Miyagun sun kashe jami'an ƴan sanda guda biyu a wani shingen bincike tare da sace shanu sama da 200
- Mazauna yankin sun bayyana cewa ƴan ta'addan waɗanda yawansu ya fi guda 50 sun kai harin ne a saman babura
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kebbi - Wasu ƴan bindiga da ake zargin ƴan ta’addan Lakurawa ne sun kashe ƴan sanda biyu a jihar Kebbi.
Ƴan ta'addan na Lakurawa a yayin harin sun kuma sace shanu sama da 200 a ƙauyen Natsini da ke ƙaramar hukumar Argungu a jihar Kebbi.
Ƴan Lakurawa sun kai hari a Kebbi
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 11:00 na dare.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni daga ƙauyen sun bayyana cewa, ƴan sandan suna a wajen wani shingen binciken ababan hawa da ke kan titin Augie/Kangiwa, lokacin da lamarin ya auku.
Ƴan ta’addan da yawansu ya kai 50 a kan babura sun kai musu hari inda suka kashe biyu daga cikinsu kafin su shiga ƙauyen su sace shanu.
Ƙauyen Natsini yana kan titin Augie/Kangiwa sannan yana da tazarar kilomita biyar daga garin Argungu.
Wani ɗan yankin mai suna Abubakar Augie ya bayyana cewa shanun da aka sace na wani fitaccen ma’aikacin gwamnati ne mai suna Lawali Black.
"Ƴan Lakurawan sun fi 50 akan babura, bayan sun ci ƙarfin ƴan sandan da ke shingen binciken, sai suka je inda aka ajiye shanun a cikin gonarsa, suka tafi da su."
- Abubakar Augie
Me hukumomi suka ce kan lamarin?
Shugaban karamar hukumar Argungu, Aliyu Gulma ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce tuni majalisar ƙaramar hukumar ta gudanar da taron tsaro kan lamarin, kuma gwamnatin jihar ta umarci jami’an tsaro da su bi sahun ƴan ta’addan da nufin ƙwato shanun da aka sace.
Ba a samu jin ta bakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Kebbi ba, SP Nafiu Abubakar, har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.
Babu sansanin ƴan bindiga a Kebbi
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris ya ba da tabbacin cewa babu wani sansanin ƴan bindiga da aka samae a jihar.
Gwamna Nasir Idris ya bayyana cewa galibin ƴan bindigan da ke yin ta'asa a jihar Kebbi, suna shigo wane daga jihohin da suke makwabtaka da ita.
Asali: Legit.ng