"Ba Kunya": Gwamna a Arewa da Magabacinsa Sun Tiƙa Rawa a Gaban Sarki, Bidiyo Ya Fito
- Tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello ya ba da nishaɗi a fadar mai martaba sarkin Ebira watau Ohinoi na Ebiraland
- A wani faifan bidiyo da ke yawo an ga Yahaya Bello tare da Gwamna Ododo suna tiƙar rawa cikin farin ciki a gaban basaraken
- Wannan dai na zuwa ne bayan tsohon gwamnan ya samu ƴanci daga gidan yarin Kuje sakamakon cika sharuɗɗan belin da kotu ta ba shi
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kogi - Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ba da nishaɗi a fadar Ohinoi na Ebiraland yayin da aka ga ya kama tiƙa rawa a gaban sarki.
Tsohon gwamnan da magajinsa, Ahmed Usman Ododo, waɗanda suka tsaya kusa da sarkin Ebiraland, an gan su a wani bidiyo suna tiƙar rawa tare da rera waƙar farin ciki.
Yahaya Bello da Ododo sun yi rawa a Kogi
Jaridar The Cable ta wallafa faifan bidiyon da aka ga Gwamna Ododo da uban gidansa, Yahaya Bello suna rawa suna rera wata waƙa da maza suka yi a harshen Ebira.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Ya Allah, muna gode maka bisa abin da ka yi mana,” in ji jiga-jigan biyu a lokacin da suka bin salon waƙar a harshen Ebira tare da mutanen da ke cikin fadar.
Yahaya Bello dai na fuskantar tuhuma daga hukumar yaki da cin Hanci da rashawa ta kasa watau EFCC.
Hukumar EFCC ta saka Yahaya Bello a gaba
EFCC na zargin tsohon gwamnan da hannu a yin sama da faɗi da kudi Naira biliyan 110,446,470,089 a lokacin mulkinsa a Kogi.
Hakan dai ya saba wa sashen 96 da 311 na dokar laifuka ta Penal Code Cap.89, da kundin dokokin Arewacin Najeriya, 1963.
Ranar 27 ga watan Nuwamba, 2024 EFCC ta gurfanar da Bello da mutum biyu da ake tuhumarsu tare, Umar Shoaib Oricha da Abdulsalami a gaban babbar kotun tarayya mai zama a Abuja.
Hukumar EFCC ta tuhume su da aikata laifuffuka 16 da suka shafi karkatar da kuɗi kimanin Naira biliyan 110.
Yadda kotu ta bayar da belin tsohon gwamnan
A ranar 10 ga Disamba, Mai shari’a Maryann Anenih, wacce ke jagorantar shari’ar, ta dage zaman zuwa 29 da 30 ga Janairu da kuma 25 da 27 ga Fabrairu bayan ta ƙi amincewa da buƙatar belin Yahaya Bello.
Daga nan jami'an tsaro suka tasa ƙeyar tsohon gwamnan zuwa gidan yarin Kuje da ke Abuja kafin zama na gaba.
Sai dai daga bisani ya samu beli kuma tsohon gwamnan ya fito daga gidan yarin Kuje bayan cika sharuɗɗan belinsa ranar 20 ga watan Disamba.
Wannan dai kamar yadda ake hasashe shi ne maƙasudin da Yahaya Bello ya tiƙa rawa a fadar sarkin tare da Gwamna Ododo don nuna farin ciki.
Yahaya Bello ya ba ƴan Najeriya hakuri
A wani labarin, kun ji cewa Yahaya Bello ya roƙi al'ummar jihar Kogi su marawa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da ta Ahmed Ododo baya don cimma nasara.
Tsohon gwamnan ya buƙsci ƴan Najeriya su ksra hakuri da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu yayin da taje kokarin magance matsaloli.
Asali: Legit.ng