Matasa Sun Lakadawa Basarake Duka kan Nada Limamin Juma'a, an Ceto Rayuwarsa
- Matasa a Ido-Osun a jihar Osun sun lakada wa sabon sarki duka kan nada sabon limami da ya jagoranci sallar Juma'a
- Oba Olaiya ya zama sarki ba tare da amincewar al’ummar Ido-Osun ba, hakan ya haifar da rikici tsakanin sassan biyu
- Rundunar 'yan sanda ta ceci sarkin daga matasan, amma har yanzu ba a samu cikakken bayanin daga gwamnati ko 'yan sanda ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Osun - An lakada wa sabon sarki, Ajeniju na Halleluyah, Oba Jelili Olaiya, duka a karamar hukumar Egbedore ta jihar Osun.
Lamarin ya faru ne bayan matasan Ido-Osun sun zarge shi da nada sabon babban limamin Juma’a da gudanar da sallah a filin su.
Musabbabin lakadawa basarake dukan tsiya
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, rikici ya biyo bayan nadin Oba Olaiya a matsayin sarki ba tare da amincewar al’ummar Ido-Osun ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matasan sun bayyana rashin jin dadin su da nadin, suna zargin sarkin da yin hakan ba bisa ka’ida ba.
Bayan haka, an ce Oba Olaiya ya gina fada a filin Ido-Osun wanda hakan ya kara harzuka matasan yankin.
Yan sanda sun ceto rayuwar basaraken
Wata majiya ta ce:
“A makon da ya gabata, ya nada Ahmad Tijani a matsayin babban limami, yayin da har yanzu akwai babban limamin Ido-Osun."
"Yau kuma sun taru domin sallar Juma’a wanda sabon limamin zai jagoranta, matasan Ido-Osun sun tayar da hankali, rikicin ya kazanta, an lakada masa duka kuma ya ji rauni.”
Wani jami’in tsaro ya bayyana cewa rundunar yan sanda ta kai daukin gaggawa inda suka ceto basaraken daga matasan.
"Yan sanda sun ceci sarkin daga wurin rikicin, amma yanzu haka yana hannunsu, za a kai shi asibiti nan ba da jimawa ba saboda ya ji mummunan rauni.”
- Cewar jami'in tsaro
Sai dai har yanzu, mai ba da shawara ga gwamna kan tsaro, Samuel Ojo, ya ce ba zai yi magana ba har sai ya tattara cikakken bayani, cewar Vanguard.
Kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Osun, Yemisi Opalola, bai yi nasara ba har lokacin tattara wannan rahoton.
An zargi masarauta da cutar iyalan tsohon sarki
Kun ji cewa rigima ta barke kan shirye-shiryen birne marigayi tsohon basarake a jihar Osun saboda zargin tatsar kudi.
Ana rigimar tsakanin 'ya'yan marigayin Oba Gabriel Adekunle na Ijesa da kuma kwamitin masarauta kan birne marigayin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng