'Yan Bindiga Sun Bi Dare, Sun Sace Mutane Masu Yawa a Kaduna
- Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun yi ta'asa a jihar Kaduna ta hanyar sace mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba
- Ƴan bindigan sun bi dare sun sace mutane 16 a ƙauyen Mararraba Mazuga da ke ƙaramar hukumar Kachia
- Wasu daga cikin mutanen da aƙa sace sun tsere yayin da aka sako wasu domin su zo su karɓo kuɗaɗen fansan ragowar waɗanda ke tsare
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Ƴan bindiga ɗauke da makamai sun yi garkuwa da aƙalla mutane 16 a jihar Kaduna.
Ƴan bindigan sun yi garkuwa da mutanen ne a ƙauyen Mararraba Mazuga da ke ƙaramar hukumar Kachia ta jihar Kaduna.
Yadda ƴan bindiga suka sace mutanen
Jaridar Leadership ta ce harin a cewar wani mazaunin garin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:00 da 12:00 na daren ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa biyu daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su sun tsere, yayin da aka sako wasu mutum bakwai domin su je su samo kuɗin fansa na sauran waɗanda suke tsare.
A cewar wani mazaunin ƙauyen, wanda ya bayyana sunansa da Wayas Musa, ya ce ɗaya daga cikin mutanen da aka sako, Na’omi Kayit, ta shaida musu cewa har yanzu ƴaƴanta mata biyu na hannun ƴan bindigan.
Ya ƙara da cewa Naomi ta ce ɗaya daga cikin ƴaƴanta mata guda biyu da aka yi garkuwa da ita ɗaliba ce a ABU Zaria, yayin da ɗayar kuma take yin karatu a Togo inda yanzu ta dawo hutu Najeriya.
A halin da ake ciki, har yanzu masu garkuwa da mutanen ba su tuntuɓi iyalan waɗanda abin ya shafa ba, domin neman kuɗin fansa kafin su sako su.
Ba a ji ta bakin ƴan sandan Kaduna ba
Ƙoƙarin jin ta bakin jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan, kan lamarin bai haifar da ɗa mai ido ba.
Ba a samu layin wayarsa ba har zuwa lokacin da aka kammala haɗa wannan rahoton.
Ƴan bindiga sun sace matafiya
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da matafiya a jihar Zamfara a lokacin da suke kan hanya.
Miyagun ƴan bindigan waɗanda suka sace mutanen a kan hanyar Shinkafi zuwa Gusau, sun kuma ƙona motar da suke ciki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng