Gwamnan APC Ya Fatattaki Sakataren Gwamnati, Ya Kori Kwamishinoni, Hadimai

Gwamnan APC Ya Fatattaki Sakataren Gwamnati, Ya Kori Kwamishinoni, Hadimai

  • Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule ya sallami Sakataren Gwamnati na jihar (SSG) tare da rusa majalisar zartaswar gwamnatinsa
  • Haka kuma, Sule ya sauke dukkan hadimansa daga mukamansu a wani taron majalisar zartarwa na gaggawa da aka gudanar a Lafia
  • Rahotanni sun nuna cewa wasu na farin ciki a bangarori bayan sallamar sakataren gwamnatin da ake zargi da jawo matsalolin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Lafia, Nasarawa - Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya yi gagarumar garambawul a gwamnatinsa.

Gwamna Sule ya sanar da sallamar Sakataren Gwamnati (SSG) da kuma rusa dukkan majalisar zartaswar gwamnatinsa.

Gwamna Sule ya yi garambawul a gwamnatinsa
Gwamna Sule ya sallami sakataren gwamnati da kwamishinoni a gwamnatinsa. Hoto: Abdullahi Sule.
Asali: Facebook

Gwamna Sule ya fatattaki mukarrabansa a Nasarawa

Wannan mataki ya biyo bayan wani taron gaggawa da aka gudanar a Lafia ranar Juma’a 3 ga watan Janairun 2025, cewar The Guardian.

Kara karanta wannan

Ana fama da rikicin sarautar Kano, gwamna a Arewa ya naɗa sababbin sarakuna 7

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bugu da ƙari, Gwamna Sule ya sauke dukkan hadimansa daga mukamansu da sauran kwamishinoninsa yayin taron da aka gabatar.

Daga bisani, Gwamna Sule ya yi godiya ga dukkan wadanda abin ya shafa kan gudunmawar da suka bayar inda ya yi musu fatan alheri.

Sai dai har yanzu, ba a bayyana dalilin rushe su ba, wanda ya haifar da damuwa da ce-ce-ku-ce tsakanin al’umma.

Wannan ya jawo maganganu da tambayoyi kan abin da ya sa gwamna ya yanke wannan shawara mai nauyi, cewar Vanguard.

Wasu na murna da matakin gwamna a Nasarawa

Majiyoyi masu kusanci da gwamnan sun bayyana cewa an dade ana tsammanin wannan mataki.

Sun kuma yi hasashen cewa yawancin wadanda aka sauke ba za su sake samun damar ci gaba da aiki a gwamnati ba.

A hannu guda, rahotanni sun nuna cewa wasu mutane sun yi murna da korar sakataren gwamnati, wanda ake zargi da jawo koma baya ga ayyukan gwamnati.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya ziyarci IBB, ya bayyana abubuwan da suka tattauna a kan Najeriya

Gwamna Sule ya kori shugaban hukumar TSC

Kun ji cewa gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya dakatar da shugaban hukumar kula da harkokin malamai (TSC) da tawagarsa nan take.

Abdullahi Sule ya ɗauki wannan matakin ne bayan gano wata badaƙala a ɗaukar sababbin malamai 1,000 da ya bayar da izini.

Bayanai sun nuna cewa shugaban TSC da yan tawagarsa sun ɗauki malamai fiye da 1,000, sannan sun take dokar ɗaukar aiki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.