Gwamnan PDP Ya Tsallake Su Atiku, Ya Gayyato Tinubu Ya Kaddamar da Wasu Ayyuka

Gwamnan PDP Ya Tsallake Su Atiku, Ya Gayyato Tinubu Ya Kaddamar da Wasu Ayyuka

  • Mai girma shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu zai kai ziyarar kwana ɗaya jihar Enugu ranar Asabar, 4 ga watan Janairu, 2025
  • Sakataren gwamnatin Enugu, Farfesa Chidiebere Onyia ya ce Tinubu zai kaddamar da wasu muhimman ayyukan yayin ziyarar
  • Daga cikin ayyukan da shugaban kasar zai ƙaddamar har da asibitoci, tituna, ɗakin taro na zamani da kuma motocin sintiri

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Enugu - Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai kai ziyara ta musamman zuwa Enugu da ke Kudu maso Gabashin Najeriya gobe Asabar, 4 ga watan Janairu, 2025.

Yayin wannan ziyara ta kwana guda, shugaba Tinubu zai kaddamar da wasu muhimman ayyuka da Gwamna Peter Mbah na jam'iyar PDP ya kammala.

Gwamna Peter Mbah da Bola Tinubu.
Shugaban ƙasa, Bola Tinubu zai kai ziyarar yini guda jihar Enugu Hoto: Peter Mbah
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa hakan na kunshe ne a wata sanarwa da sakataren gwamnatin Enugu, Farfesa Chidiebere Onyia, ya fitar a ranar Juma’a.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa gwamnan Bauchi bai bi gwamoni zuwa gidan Tinubu ba

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

BolaTinubu zai ziyara jihar Enugu

Ya ce a karon farko tun bayan hawa mulki, babban kwamandan rundunar sojin Najeriya, Bola Tinubu zai kawo ziyarar yini guda ranar Asabar.

Onyia ya ce:

"Gwamnatin Enugu na farin cikin sanar da cewa shugaban ƙasa kuma babban kwamandan rundunar sojin Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, GCFR, zai kawo ziyara ta farko a ranar Asabar, 4 ga Janairu, 2025.

Ayyukan Gwamna Mbah da Tinubu zai kaddamar

Ya lissafo ayyukan da Tinubu zai kaddamar da suka haɗa da makarantu 30 da Gwamna Mbah ya kammala daga cikin 260 da aka fara ginawa a mazaɓu 260.

Sai kuma asibitocin kula da lafiya a matakin farko guda 60 da aka kammala daga cikin 260 da ake ginawa a mazabu 260 da babban dakin taro na zamani na Enugu

Sauran abubuwan da Tinubu zai kaddamar su ne cibiyar tsaro ta zamani, da kuma motocin sintiri 150 da aka shigar da kyamarorin tsaro masu fasahar zamani (AI).

Kara karanta wannan

"Ka fito ka faɗawa mutane gaskiya," Peter Obi ya kwancewa Tinubu zani a kasuwa

Sanarwar ta kara da cewa shugaba Tinubu zai kuma kaddamar da wasu titunan karkara da aka kammala yayin wannan ziyara ta rana guda.

Gwamna Mbah ya yi ƙarin albashi

Kun ji cewa Gwamna Peter Mbah ya fara biyan ma'aikatan gwamnatin Enugu sabon mafi ƙarancin albashi na N80,000.

Sai dai ƙungiyar kwadago ta koka kan tsarin da aka yi amfani da shi wajen ƙarin albashin kuma tuna ta aika kokenta zuwa ga Gwamna Mbah.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262