Amarya Ta Hada Baki da Tsohon Saurayinta Sun Saka Guba a Abincin Ango

Amarya Ta Hada Baki da Tsohon Saurayinta Sun Saka Guba a Abincin Ango

  • Rahotanni na nuni da cewa wani aure a Jihar Jigawa ya koma zaman makoki bayan zargin amarya da sanya guba a abincin ango
  • Bayanan 'yan sanda sun tabbatar da cewa an kwantar da mutane a asibiti yayin da daya daga cikin abokan ango ya rasa ransa
  • Rundunar ’yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin kuma ta kama amarya da wata mace domin bincike da kuma daukar mataki na gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Jigawa - A wani al’amari mai tayar da hankali, aure a karamar hukumar Jahun a jihar Jigawa, ya dauki sabon salo bayan zargin amarya da sanya guba a abincin bikin.

Rahotanni sun tabbatar da cewa lamarin ya yi sanadiyyar mutuwar daya daga cikin abokan ango yayin da ango ya kwanta a asibiti.

Kara karanta wannan

Daga zuwa sasanta rikicin miji da mata, an kashe wani malamin addini a Najeriya

Jigawa
Amarya ta saka guba a abincin ango a Jigawa. Hoto: Legit
Asali: Original

Rundunar ’yan sandan jihar ta tabbatar wa Legit faruwar lamarin kuma ta bayyana cewa ana gudanar da bincike domin gano musabbabin wannan abu mai tayar da hankali.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka saka guba a abincin aure

'Yan sanda sun tabbatar da cewa amaryar 'yar shekaru 15 mai suna Zahra'u Dauda ta hada baki ne da tsohon saurayinta mai suna Lawan Musa mai shekaru 22 wajen aikata laifin.

Angon mai suna Khamisu Haruna mai shekaru 29 dan karamar hukumar Jahun ne yayin da amaryar da tsohon saurayinta suka fito daga karamar hukumar Kiyawa.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Shi’isu Adam, ya bayyana cewa sun samu rahoton cewa an samu guba a abincin bikin wanda hakan ya jawo tashin hankali.

“Mun samu rahoto cewa amarya ta sanya guba a abincin bikin, inda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutum daya”

- SP Shi'isu Adam

Kakakin 'yan sandan ya kara da cewa an kama amarya tare da wata mace, kuma yanzu haka suna hannu inda ake ci gaba da bincike a sashen binciken manyan laifuffuka na rundunar.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali: Malamin addini ya sa bindiga ya harbe wani yaro har lahira

An sallami mutane daga asibiti

SP Shi’isu Adam ya tabbatar da cewa dukkannin abokan ango da suka ci abincin da aka zarga da guba sun warke bayan jinya a asibiti, sai dai mutum daya ya rasa ransa.

Punch ta wallafa cewa kakakin ya ce za su tabbatar da cewa an yi adalci a lamarin yayin da rundunar ’yan sanda ke kokarin gano cikakken abin da ya faru.

An bukaci a kwantar da hankali

'Yan sanda sun bukaci jama’a da su kwantar da hankulansu yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.

Al’amarin ya jawo ce-ce-ku-ce tsakanin al’umma, inda ake jiran sakamakon binciken da zai fayyace gaskiyar lamarin.

'Yan sanda 140 sun rasu a Abuja

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sanda a birnin tarayya Abuja ta ce ta rasa jami'ai kimanin 140 a shekara daya.

Kwamishinan 'yan sandan Abuja ya bayyana cewa rikici da 'yan Shi'a, barazanar tsaro da rashin lafiya na cikin musabbabin rasa jami'ai a 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng