Sojojin Najeriya Sun Shirya Murkushe Bello Turji da Sauran Miyagu da Suka Addabi Jama'a

Sojojin Najeriya Sun Shirya Murkushe Bello Turji da Sauran Miyagu da Suka Addabi Jama'a

  • Babban hafsan tsaron kasa, Janar Christopher Musa ya sake aika sako ga ƴan bindiga da sauran ƴan tada ƙayar baya da suka hana zaman lafiya
  • Janar Musa ya ce dakarun sojin Najeriya ba za su yi ƙasa a guiwa ba wajen tabbatar da tsaro ta hanyar murkushe miyagu a faɗin kasar nan
  • Jami'in ya kuma yabawa dakarun sojin rundunar Operation Save Heaven bisa jajircewar da suka yi don kawo karshen aikata miyagun laifuka

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna - Babban Hafsan Hafsoshin Sojin Najeriya, Janar Christopher Musa, ya jaddada aniyar dakarun sojoji na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin ƴan ƙasa.

C. Musa ya ce dakarun sojojin sun shirya tsaf domin murkushe dukkan ƙungiyoyin miyagu da suka zama barazana ga zaman lafiya da tsaro.

Janar Christopher Musa.
Rundunar sojoji ta jaddada aniyarta na murkushe duk wata barazanar tsaro a Najeriya Hoto: Defence Headquaters Nigeria
Asali: Facebook

Ya faɗi haka ne da yake zantawa da ‘yan jarida yayin ziyarar da ya kai sansanin sojoji a karamar hukumar Zangon Kataf a jihar Kaduna, Channels tv ta rahoto.

Kara karanta wannan

"Babu sauran sansanin ƴan bindiga a jihata," Gwamna a Arewa ya cika baki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rundunar sojoji ta samar da kayan aiki ga sansanin sojin don magance matsalolin tsaro a Kudancin Kaduna da kewaye.

Hafsan tsaro ya yabawa sojojin Najeriya

Babban hafsan tsaron ya yabawa gwarazan sojojin bisa sadaukarwa da jajircewar da suke yi a harkar tsaron ƙasa tare da tabbatar masu za a inganta walwalarsu.

Ya kuma bukaci sojoji da su kasance masu taka tsan-tsan da kwarewa wajen kare kasa da kuma mutunta hakkin dan Adam wajen gudanar da ayyukansu.

Janar Christopher Musa ya jaddada muhimmancin hada kai da sauran hukumomin tsaro da fararen hula wajen cimma burin tabbatar da tsaron kasa.

An bukaci dakarun sojoji su kara dagewa

A nasa jawabin, kwamandan rundunar sojin Operation Safe Haven, Manjo Janar Abdulsalam Abubakat ya bukaci sojojin su kare zage dantse a yakin da suka tasa a gaba.

Ya kuma ƙara wa dakarun sojojin kwarin guiwar domin samun nasara a aikin wanzar da zaman lafiya a yankinsu.

Kara karanta wannan

"Ka fito ka faɗawa mutane gaskiya," Peter Obi ya kwancewa Tinubu zani a kasuwa

Bello Turji ya kusa zama marigayi

A wani rahoton, kun ji cewa hedkwatar tsaro ta ce Bello Turji da sauran hatsabiban ƴan ta'adda za su girbi abin da suka shuka nan kusa.

DHQ ta bayyana cewa dakarun sojoji za su ga bayan Turji kamar yadda suka sheke shugabannin ƴan ta'adda sama da 1,000 a Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262