Ana Fama da Rikicin Sarautar Kano, Gwamna a Arewa Ya Naɗa Sababbin Sarakuna 7

Ana Fama da Rikicin Sarautar Kano, Gwamna a Arewa Ya Naɗa Sababbin Sarakuna 7

  • Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya naɗa wasu sababbin sarakuna a masarautu bakwai da ya kirkiro a jihar Adamawa
  • Mai girma Ahmadu Fintiri ya taya sababbin sarakunan murna tare da rakon su zama masu gaskiya da rikon amana a mulkinsu
  • Wannan dai na zuwa ne bayan kirkiro masarautu bakwai a Adamawa, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce kan karfin ikon Lamido

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Adamawa - Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya amince da naɗin sababbin sarakuna bakwai na masarautun da ya kirƙiro a jihar Adamawa.

Babban sakataren watsa labaran gwamnan, Humwashi Wonosikou, shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma'a, 3 ga watan Janairu, 2025.

Gwamna Ahmadu Fintiri.
Gwamna Ahmadu Fintiri ya nada sababbin sarakuna 7 a jihar Adamawa Hoto: @followADSG
Asali: Twitter

Gwamnatin jihar Adamawa da ke Arewa maso Gabas ta wallafa sanarwar mai ɗauke da sunayen sababbin sarakunan a shafinta na manhajar X.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya fatattaki sakataren gwamnati, ya kori kwamishinoni, hadimai

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Fintiri ya kirkiro masarautu 7

Idan baku manta Gwamna Ahmadu Fintiri ya kirkiro sababbin masarautu bakwai a faɗin jihar Adamawa a makonnin da suka gabata.

Lamarin dai ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin al'ummar jihar, inda wasu ke ganin wannan duk wani shiri ne na rage karfin Lamidon Adamawa.

Sai dai tuni gwamnatin Fintiri ta musanta raɗe-raɗi, tana mai cewa ta kirkiro masarautun ne domin ƙara faɗaɗa ayyukan sarakuna a lungu da sakon Adamawa.

Jerin sababbin sarakunan Adamawa

A yau Juma'a, Gwamna Fintiri ya amince da mutum bakwai da aka zaɓa a matsayin sababbin sarakunan da za su mulki yankunan masarautun.

1. Mai martaba Alhaji Sani Ahmadu Ribadu - Sarkin Fufore.

2. Mai martaba Barista Alheri B. Nyako - Tol na masarautar Huba

3. Mai martaba Farfesa Bulus Luka Gadiga - Mbege Ka na masarautar Michika

4. Mai martaba Dr Ali Danburam (MBBS, FWACP, FCCP) - Ptil na masarautar Madagali

Kara karanta wannan

Peter Obi ya ziyarci IBB, ya bayyana abubuwan da suka tattauna a kan Najeriya

5. Mai martaba Aggrey Ali - Kumu na masarautar Gombi

6. Mai martaba Ahmadu Saibaru - Sarkin Maiha

7. Mai martaba John Dio: Gubo na masarautar Yungur.

Gwamna Fintiri ya taya sarakunan murna

Gwamnan ya taya sabanbin sarakunan murna, ya jaddada cewa ya zaɓe su ne bisa cancanta da kuma farin jinin da suke da shi a tsakanin jama’a.

Ahmadu Fintiri ya bukace su da su kasance masu gaskiya da rikon amana a ayyukan da aka ɗora masu, ya ce naɗin zai fara aiki nan take.

Majalisa ta musanta rage ikon Lamidon Adamawa

Kun ji cewa Majalisar dokokin jihar Adamawa ta musanta jita-jitar da ake yaɗawa cewa sabuwar dokar masarautun da ta zartar za ta rage ikon Lamidon Adamawa.

Majalisar dai ta amince da kudirin kirkiro masarautu da Gwamna Amadu Fintiri ya aika mata, lamarin da ya jawo zargin gwamnatin jihar tana da wani shiri a ƙasa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262