"Babu Sauran Sansanin Ƴan Bindiga a Jihata," Gwamna a Arewa Ya Cika Baki
- Gwamnan Kebbi, Dr. Nasir Idris ya gana da shugabannin tsaro domin fara shirye-shiryen magance matsalar tsaro a sabuwar shekara
- Ƙauran Gwandu ya ce babu sansanin ƴan bindiga ko ɗaya a jihar Kebbi, daga makotan jihohi suke shigowa su aikata ta'addanci
- Gwamnan ya ce zai samar da ƙarin kayan aiki ga ƴan banga domin inganta ayyukansu na taimakawa jami'an tsaron Najeriya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kebbi - Gwamna Nasir Idris Kauran Gwandu ya bayyana cewa babu sansanin ƴan bindiga ko ɗaya da aka kafa a faɗin jihar Kebbi.
Gwamna Nasir ya yi bayanin cewa galibin ƴan bindigar da ke aikata ta'addanci a jihar suna shigowa ne daga jihohin makwafta a shiyyar Arewa maso Yamma.
Yan bindiga na shiga Kebbi su yi ta'addanci
Ya ce Kebbi ta haɗa boda da jihohi uku da kuma kasashe biyu, wanda hakan ya sa miyagu ke shigowa su aikata mugun nufinsu, kamar yadda Channels tv ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Nasir Idris ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan wani taron tsaro da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Birnin Kebbi.
Ya jaddada cewa gwamnatin jihar Kebbi ta yi kokari matuka wajen magance matsalolin tsaro a cikin shekarar da ta gabata watau 2024.
Makasudin taron tsaron da aka yi, in ji gwamnan shi ne tsara dabaru da tsare-tsaren tunkarar shekarar 2025.
Gwamna Nasir zai farfaɗo da ƴan banga
Ƙauran Gwandu ya ce gwamnatinsa za ta kara inganta ayyukan ƴan banga a ƙoƙarin kawo karshen ayyukan ƴan bindiga da sauran miyagu a Kebbi.
Gwamnan Kebbi ya kuma jaddada cewa ƴan banga suna matuƙar kokari wajen taimaka wa jami'an tsaro a yaƙi da ƴan tada ƙayar baya.
"A wani bangare na taimaka masu, gwamnati za ta sayo babura 1,000 ga kungiyoyin ’yan banga don inganta ayyukansu yadda ya kamata," in ji shi.
Gwamnan Kebbi ya raba babura ga ma'aikata
A wani rahoton, an ji cewa Gwamna Nasir Idris ya raba babura ga ma'aikatan gidan gwamnatinsa domin saukaka masu zuwa wurin aiki.
Ya ce ya ɗauki wannan matakin ne domin karawa ma'aikatan kwarin guiwar ci gaba da kokarin sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng