Farashin Fetur Zai Sake Sauka, Dangote da Kamfanonin Mai Sun Kulla Wata Yarjejeniya
- Matatar Dangote da ke birnin Legas ta kulla yarjejeniya da kamfanin Ardova da Heyden domin samar da fetur mai araha
- Irin wannan yarjejeniyar ta sayen mai da yawa ce ta taimaka wajen rage farashin litar fetur zuwa N935 a gidajen mai na MRS Oil
- Dangote ya taimaka wajen magance ƙarancin mai ta wannan dabarar a lokacin bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Matatar Dangote ta bayyana cewa ta kulla yarejejeniya da kamfanin Heyden Petroleum da Ardova Plc domin samar da man fetur mai araha a Najeriya.
Matatar ta ce haɗin gwiwar ta yiwu ne saboda sauƙin tattalin arziki da aka samu sakamakon tsarin musayar danyen mai da kudi da shugaba Bola Tinubu ya kawo.
Tasirin yarjejeniyar Dangote da kamfanoni
Matatar Dangote ta ce yarjejeniyar sayen mai da yawa daga gare su zai tabbatar da isasshen mai a farashi mai sauƙi ga 'yan Najeriya, inji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan ci gaba ya biyo bayan matakin da kamfanin MRS Oil ya ɗauka na shiga yarjejeniya makamanciyar haka da matatar Dangote.
A sakamakon haka, kamfanin MRS Oil ya rage farashin mai zuwa N935 a kan kowace lita a gidajen mansa na ƙasa baki ɗaya.
An kulla yarjejeniyar samar da fetur da araha
Matatar Dangote ta ce wannan saukin farashi ya taimaka wajen magance bambance-bambancen farashin mai tsakanin jihohi.
Yarjejeniyar sayen mai da yawa tsakanin Dangote, Ardova da Heyden zai taimaka wajen samar da isasshen mai a farashi mai sauki, wanda zai amfani al’ummar ƙasar.
Jaridar ThisDay ta rahoto kamfanin Ardova ya ce wannan yarjejeniya za ta ƙarfafa gasa a fannin mai da iskar gas na ƙasa baki ɗaya.
Dangote ya bayyana cewa wannan haɗin gwiwa zai samar da tsari mai dorewa wanda ke amfani wa bangarorin da ke cikin yarjejeniyar.
Dangote ya saukakawa 'yan Najeriya a 2024
Matatar Dangote wadda ta fara aiki a 2024, ta taka rawar gani wajen magance ƙarancin mai tare da rage matsalolin da ke haifar da tashin farashin man a kasar nan.
A lokacin bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara kuwa, ’yan Najeriya sun ji daɗin samun mai a kowane lokaci ba tare da tashin farashi ba.
Wannan haɗin gwiwa na Dangote da kamfanonin mai zai tabbatar da zaman lafiya a kasuwar mai tare da tabbatar da wadatar man fetur ga kowa.
'Yan kasuwa sun fara dakon feturin Dangote
A wani labarin, mun ruwaito cewa kungiyar IPMAN ta fara dakon man fetur kai tsaye daga matatar Ɗangote a Legas bayan cimma yarjejeniya tsakanin su.
Sakataren yaɗa labaran IPMAN, Chinedu Ukadike, ya tabbatar da wannan ci gaban, yana mai cewa hakan zai sauƙaƙa samar da man fetur.
A halin yanzu, ƴan kasuwar IPMAN na kuma amfani da kamfanin MRS Oil wajen dakon fetur domin tabbatar da wadatar sa a fadin kasar nan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng