"Ba Karya Muke ba," NNPCL Ya Gayyaci Obasanjo Matatun da Aka Gyara a kan $2bn
- Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya samu gayyatar kamfanin mai na kasa (NNPCL) zuwa matatunsa
- Gayyatar na zuwa ne bayan Cif Obasanjo ya yi zargin cewa akwai alamun tambaya a sahihancin gyaran matatun
- A shekarar 2024 ne kamfanin mai na kasa da gwamnatin tarayya su ka bayyana farfado da matatun Fatakwal da Warri
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos - Kamfanin main a kasa (NNPCL) ya gayyaci tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo don duba matatun man da aka gyara a shekarar 2024.
Wannan martani ne ga shakkun da Cif Obasanjo ya bayyana a kan ingancin gyaran farfado da matatun Fatakwal da Warri, inda aka kashe $2b a kan gyaran su
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa babban jami’in hulda da jama’a na NNPCL, Mista Olufemi Soneye, ya jinjina wa matsayin tsohon shugaban kasar da gudunmawarsa ga ci gaban kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Martanin kamfanin NNPCL ga Obasanjo
Rediyo Najeriya ta wallafa cewa kamfanin mai na NNPCL ya tabbatar da cewa ba a kashe $2bn wajen wajen gyaran matatun Fatakwal da Warri ba.
Kakakin kamfanin na kasa, Olufemi Soneye ce:
“Muna girmama tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo a matsayin daya daga cikin dattawan kasa da suka ba da gudunmawa mai yawa ga ci gaban Najeriya.
"Muna matukar daraja ra’ayinsa. Duk da haka, muna so mu jaddada cewa NNPC ta samu gagarumin canji.”
‘An samu ci gaba a NNPCL,” Soneye
Kamfanin NNPCL ya bayyana cewa yanzu ya canja daga mai daukar asara zuwa guda daga cikin masu jagoranci kasuwancin makamashi na duniya.
Ya danganta nasarorin da aka samu ga jagorancin shugaban kamfanin, Mele Kyari da kuma manufofin sauyin makamashi na Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Soneye y ace;
“Muna maraba da tsohon Shugaba Obasanjo don duba matatun da aka gyara. Hikima da gogewarsa ba za su misaltu ba, kuma muna matukar daraja shawarwarinsa."
Obasanjo ya yi magana kan NNPCL
A baya, mun ruwaito cewa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa gwamantin Marigayi Umar Musa 'Yar'adua ya ki amincewa da tayin Dangote a NNPCL.
Obasanjo ya bayyana yadda shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote ya samar da tawaga da tayin ba shi damar gudanar da NNPCL a kan $750m, amma gwamnati ta ki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng