Rikicin 'Yan Shi'a da Saurasu Sun Jawo Mutuwar 'Yan Sanda 140 a Abuja
- Kwamishinan ‘Yan Sandan Abuja, Olatunji Rilwan Disu, ya bayyana cewa wasu daga cikin jami’ansa 140 sun rasu sakamakon tashin-tashina a 2024
- Olatunji Rilwan Disu ya ce wasu jami’an sun rasu ne a bakin aiki, yayin da wasu suka rasu a gidajensu sakamakon hawan jini da sauran matsalolin lafiya
- CP Disu bayyana cewa wasu daga cikin iyalan marigayan sun samu hakkokinsu bisa kokarin rundunar tare da goyon bayan IGP Kayode Egbetokun
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kwamishinan ‘Yan Sandan Birnin Tarayya Abuja, Olatunji Rilwan Disu ya bayyana yadda matsalolin tsaro da na lafiya suka yi sanadiyyar rasuwar wasu jami’ansa 140 a 2024.
CP Disu ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da manema labarai ranar Alhamis, inda ya ce jami’an sun rasu ne a yayin da suke yi wa kasa hidima.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa rundunar ta tabbatar da biyan hakkokin wasu daga cikin iyalan wadanda suka rasu.
Rikicin 'yan Shi'a da mutuwar 'yan sanda
CP Disu ya bayyana cewa wasu jami’an sun mutu sakamakon tashe-tashen hankula da suka hada da zanga-zangar ‘yan Shi’a da sauran tashin-tashina.
“A yau ma kawai, mun rasa wani jami’inmu wanda ya kwanta barci bai kuma tashi ba. Hakan yana nuna irin yadda jami’anmu ke rasuwa yayin da suke aiki domin kare ƙasar nan,”
- CP Olatunji Rilwan Disu
Ya kara da cewa wasu jami’ai sun rasu ne sakamakon faɗuwa haka kawai da rashin lafiya yayin da suke bakin aiki.
Biyan hakkokin iyalan 'yan sanda
The Nation ta rahoto cewa CP Disu ya bayyana cewa rundunar ‘yan sandan ta biya wasu daga cikin iyalan jami’an da suka rasu hakkokinsu tare da musu wata alfarma ta musamman.
CP Disu ya ce an samu biyan hakkokin ne bisa jagorancin Sufeto Janar na 'Yan Sanda, Kayode Egbetokun.
'Yan sanda za su cigaba da kare Abuja
Kwamishinan ya jaddada cewa rundunar za ta ci gaba da fadada shirinta na wayar da kan jama’a domin magance kalubalen tsaro da ke kunno kai a Abuja.
Ya ce za su yi amfani da nasarorin da suka samu a 2024 domin ganin sun ci gaba da samun zaman lafiya da tsaro a Abuja a shekarar 2025.
An kama masu laifi 2,425 a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Kano ta bayyana manyan nasarorin da ta samu wajen kawar da barna a 2024.
Kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Salman Dogo Garba ya bayyana cewa sun kama masu laifi daban daban da suka kai 2,425 a shekarar da ta wuce.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng