An Shiga Tashin Hankali a Gombe yayin da Hatsarin Mota Ya Yi Ajalin Sama da Mutum 5

An Shiga Tashin Hankali a Gombe yayin da Hatsarin Mota Ya Yi Ajalin Sama da Mutum 5

  • Hatsarin mota a kan titin Kaltungo-Cham ya yi sanadin mutuwar mutane bakwai, yayin da 31 suka samu raunuka daban-daban
  • Hukumar kiyaye hadurra ta jihar Gombe ta danganta hatsarin da matsalar birki, wanda ya jawo kifewar tirela dauke da mutane 38
  • FRSC ta gargadi mutane da su guji hawa tirela ko manyan motoci da nufin yin tafiye-tafiye, "domin an yi su ne don daukar kaya kawai"

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Gombe - Mutane bakwai sun rasa rayukansu a wani hatsari da ya rutsa da mota daya tilo a kan titin Kaltungo – Cham a jihar Gombe.

Mista Samson Kaura, kwamandan hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) a jihar, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Alhamis.

Hukumar FRSC ta yi magana yayin da hatsarin mota ya yi ajalin mutum 7 a Gombe
Hukumar FRSC ta gargadi masu hawa tirela yayin tafiye tafiye bayan hatsarin Gombe. Hoto: @FRSCNigeria
Asali: Facebook

Hatsarin mota ya yi ajalin mutum 7

Jaridar Daily Trust ta rahoto Mista Kaura na cewa mutane 31 sun samu raunuka iri-iri a hatsarin motar, wanda ya faru da misalin karfe 7:30 na safe.

Kara karanta wannan

"Wuce gona da iri," Dattawan Arewa sun ce a biya diyyar wadanda sojoji suka hallaka a Sakkwato

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mista Kaura ya danganta hatsarin da matsalar birki, inda tirela dauke da lemu da mutane 38, ciki har da maza 34, mata biyu da yara biyu ta wuntsula.

Ya bayyana cewa wadanda suka rasu sun hada da maza biyar, mace daya da yaro daya.

FRSC ta gargadi mutane kan hawa tirela

Haka zalika an garzaya da gawarwakin mutanen bakwai zuwa asibitin Kaltungo, yayin da 31 ke samun kulawar likitoci.

Kaura ya gargadi 'yan Najeriya da su daina hawa tirela don gujewa biyan kudin motar haya, yana cewa, “kudin da ake biya na hawa tirela bai kai darajar rai ba.”

Ya kara da cewa:

"Hatsari daya tilo amma mun samu mutane da dama da suka rasa rayukansu da samun raunuka. Mun kwashe ranar baki daya muna kula da lamarin."

FRSC ta gargadi direbobi kan kiyaye hadura

Hukumar FRSC ta yi kira ga jama’a da su daina amfani da tirela ko manyan motoci don tafiye tafiyensu saboda gudun biyan kudin mota mai tsada.

Kara karanta wannan

Yadda aka kashe 'yan bindiga 40, aka kama miyagu 916 a jihar Katsina

“Don Allah ku daina hawa tirela ko manyan motoci. An yi su ne don daukar kaya ba don mutane ba."

- A cewar Mista Kaura.

Kaura ya kuma shawarci direbobi da su kula da gyaran motocinsu yadda ya kamata don rage yawan hadura a kan titunan jihar da ma kasa baki daya.

Hatsarin mota ya rutsa da tawagar gwamna

A wani labarin, mun ruwaito cewa hatsarin mota ya rutsa da ayarin motocin gwamnan Benue, Hyacinth Alia, kamar yadda wasu mazauna yankin suka tabbatar.

Rahotanni sun bayyana cewa mutum guda ya rasa ransa a hatsarin, lamarin da ya tada hankula a yankin Ihugh da ke ƙaramar hukumar Vandeikya a jihar Benue.

Duk da haka, wani hadimin gwamnan ya musanta cewa ayarin motocin gwamnan ne suka yi hatsarin da ya jawo mutuwar wannan mutum.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.