Satar Waya: 'Yan Sanda Sun Yi Tara Tara, An Damke Shamsiyya da Yaranta a Kano
- Dankwali ya ja hula a wajen aikata mugun aikin satar wayoyin hannu a unguwar Kano da ke fama da matsalar kwacen salula
- Rundunar 'yan sandan jihar ta fito a yammacin Alhamis da labarin damke matashiya, Shamsiyya Yusuf Adamu da yaranta
- Jami'in hulda da jama'a na rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana adadin wayoyin da aka kama a hannun zugar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Rundunar ‘yan sandan Kano ta baro da wata zugar barayin waya ta mutane biyar da suka kware wajen satar wayoyin hannun jama’a a unguwanni daban-daban.
Rundunar ta cafke matashiya Shamsiyya Adamu, ‘yar shekara 19, da ke zaune Brigade Quarters Kano, tun a ranar 21 Disamba, 2024, bayan bincike.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa an kama ta ne bayan rahotanni na sace wayoyi a Unguwa Uku.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
‘Yan sandan Kano sun samu korafi
Rundunar ‘yan sandan Kano ta tabbatar da saun korafi daga mazauna birnin Kano kan wata budurwa da ke sace wayoyin hannu har shaguna da gidajen jama’a.
Rahotannin sun nuna cewa tana amfani da direban Adaidaita Sahu da kuma dan damfara a yanar gizo wajen aiwatar da laifin, sannan ta yi layar zana abinta.
Rundunar ‘yan sandan Kano ta farauto Shamsiyya
Kwamishinan ‘yan Sanda na Jihar Kano, CP Salman Dogo Garba, ya kafa tawaga ta musamman domin ta shiga farautar matashiyar da ake zargi da satar waya, Shamsiyya Adamu.
Bayan jagorarsu Shamsiyya, rundunar ta bayyana kama wasu mutum hudu ciki har da direban Keke Napep dinta ma shekaru 23, Idris Adamu.
Sauran sun hada da Al’asan Dahiru, mai shekara 24, wanda ke kula da sayar da wayoyin da aka sato.
Akwai Abdulmajid Haruna, mai shekara 27 da ke sayen wayoyin satar, Salim Auwalu, mai shekara 21 da ke cire kudi daga asusun jama’a.
Rundunar ‘yan sanda ta kwato kayan sata
Rundunar ‘yan sandan Kano ta bayyana kwato wayoyin salula guda shida daga hannun wadanda ake zargi, kuma ana ci gaba da kokarin kwato sauran kayayyakin sata.
Har yanzu, mutane 30, ciki har da mata 29 da namiji daya, sun yi korafi kan Shamsiyya, wadda ta amsa laifin sata a lokuta daban-daban a shekarar 2024.
'Yan sandan Kano sun cafke 'yan fashi
A wani labarin, mun ruwaito yadda rundunar 'yan sandan Kano ta ce an samu nasarori wajen yaki da miyagun ayyuka da damke wasu daga cikin masu aikata su a shekarar 2024.
Kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Salman Dogo ya bayyana cewa an kama an kama 'yan fashi 189, masu gaa mutane 39 da 'yan daba akalla 1,987, duk a shekarar da ta kare.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng