'Ku Dage da Addu'a;" Malamin Addini Ya Hango Abin da Zai Faru da Najeriya a 2025
- Malamin addini, Samuel Ojo ya ce 2025 za ta zama shekara ta kwanciyar hankali, samun sauki da ci gaban 'yan Najeriya
- Ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su kasance masu kyakkyawan yakini yana mai cewa matsalolin kasar ba za su gagari Allah ba
- Malamin ya jaddada cewa idan 'yan kasar suka dage da addu'a, to matsalolin tattalin arziki, rashin tsaro za su zama tarihi a bana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ibadan - Shugaban Cocin Freedom Apostolic Revival International Ministries, Samuel Adebayo Ojo, ya hango lokacin da wahalhalun da suka addabi Najeriya za su kare.
A lokacin wani taron shekara-shekara a garin Ori Oke Ogo da ke Asejire kusa da Coca-Cola, Ibadan, malamin ya tabbatar da cewa akwai tarin alheri a 2025.
Malamin addini ya hango wa Najeriya sauki
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa dubunnan masu ibada sun halarci taron kai tsaye, yayin da miliyoyi suka kalla ta kafar yanar gizo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin hudubar da ya gabatar, Fasto Samuel Ojo ya bayyana hangen nesansa game da makomar kasar nan, yana mai cewa:
“Ubangiji ya nuna mani cewa 2025 za ta zama shekara ta kwanciyar hankali ga Najeriya. Za a samu saukin wahalhalu da matsalolin kasar nan."
"Allah Ya ji kukanmu" - Malamin addini
Ya kara da cewa wannan shekarar za ta kasance lokacin farfadowa, waraka da ci gaba, tare da bukatar kowa ya kasance mai kyakkyawan yakini.
“Mun yi kuka a matsayin kasa, kuma Allah ya ji kukanmu. Lokacin kuka ya kare; yanzu lokacin sake gina kasa da hadin kai ne."
- A cewar malamin.
Fasto Samuel Ojo wanda sananne ne a Najeriya a bangaren hangen nesa da ayyukan taimakon al’umma, ya samu karbuwa sosai a tsakanin al'ummar Kirista.
Najeriya na fama da matsaloli daban daban
Wannan hasashen nasa na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke fama da wahalhalu, ciki har da hauhawar farashin kayayyaki da rashin aikin yi.
An rahoto cewa hakan na faruwa ne sakamakon tasirin tattalin arziki na duniya, wanda ya kara jefa kasar cikin mawuyacin hali.
Matsalolin tsaro, daga ta’addanci a Arewa maso Yamma zuwa tashe-tashen hankula a Kudu maso Gabas, sun sanya mutane cikin damuwa.
Malamin addini ya aika sako ga shugabanni
A lokaci guda, hauhawar farashin rayuwa ya jefa miliyoyin mutane cikin talauci, wanda ya haddasa zanga-zanga da karin wahalhalu.
A kan hakan ne Fasto Ojo ya bukaci ‘yan Najeriya da su kasance masu addu’a da sanya kwarin gwiwa, yana mai cewa matsalolin kasar ba za su gagari Allah ba.
Ya kuma nuna goyon bayansa ga hadin kan kasa da adalci a cikin al’umma, yana kira ga shugabanni da su bullo da tsare-tsaren da za su saukaka wa talaka.
Malami ya hango matsalar da ke jiran Najeriya
A wani labarin na daban, mun ruwaito cewa fitaccen malamin addini, Primate Elijah Ayodele ya hango wata gagarumar matsala da Najeriya za ta fuskanta a 2025.
A wani faifan bidiyo, Primate Ayodele ya jaddada cewa Najeriya za ta fuskanci matsanancyar hauhawar farashin kayayyaki da ba ta taba gani ba a baya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng