Hukumar NDLEA Ta Cafke Sama da Mutane 1,345 a Jihar Kano, Ta Bayyana Laifuffukansu
- Hukumar NDLEA ta kama mutane 1,345 da kwace kilogram 8.4 na kwayoyi, ciki har da tramadol miliyan biyar a jihar Kano
- Hukumar ta rushe sansanonin kwayoyi 20 tare da gudanar da gwajin kwayoyi ga mutane 1,114 masu neman shugabanci a jihar
- Shugaban NDLEA na Kano, Abubakar Idris-Ahmad ya yi bayanin irin nasarorin da hukumar ta samu a 2024 da ta gabata
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Hukumar NDLEA ta jihar Kano ta kama mutane 1,345 tare da kwace kilogram 8,430.239 na miyagun kwayoyi a shekarar 2024.
Kwamandan hukumar na Kano, Abubakar Idris-Ahmad, ya bayyana haka ranar Alhamis yayin hira da manema labarai a jihar.
2025: NDLEA ta kama mutane 1,345 a Kano
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito Abubakar yana cewa daga cikin wadanda aka kama, akwai maza 1,301 da mata 44.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idris-Ahmad ya ce kwayoyin da aka kwace sun hada da tabar wiwi, hodar iblis, methamphetamine, codeine da fiye da kwayoyi miliyan biyar na tramadol.
Ya ce hukumar ta samu damar gurfanar da mutane 128 da aka yanke masu hukunci kan laifukan da suka shafi sha da fataucin kwayoyi daban-daban.
NDLEA ta rushe sansanonin safarar kwayoyi
Idris-Ahmad ya ce:
“Mun fara shirin ‘Operation Hana Maye’ don magance matsalar shan miyagun kwayoyi da tabbatar da tsaro ga al’ummar Kano."
Haka zalika, ya shaida cewa hukumar ta rushe sansanonin sayar da kwayoyi fiye da 20 a wurare daban-daban na jihar Kano.
Wuraren da aka rushe sansanonin sun hada da filin Idi, Dan Agundi, cibiyar matasa ta Sani Abacha da filin wasanni na Sani Abacha.
Matasa 101 sun daina shan kwayoyi a Kano
Ya bayyana cewa an gudanar da gwaje-gwajen kwayoyi ga mutane 1,114 da suka nemi tsayawa takarar shugabancin kananan hukumomi don tabbatar da shugabanci nagari.
Haka kuma, hukumar ta yi atisayen wayar da kan jama'a kan illolin kwayoyi da gwaje gwaje ga matafiya domin dakile safarar miyagun kwayoyi.
Idris-Ahmad ya ce matasa 101 da suka tsunduma cikin shan kwayoyi sun shiryu yanzu tare da dawowa cikin al’umma ta hanyar shirin hukumar, inji rahoton Premium Times.
NDLEA ta godewa gwamnatin Kano
Ya godewa shugaban NDLEA na kasa Mohammed Buba-Marwa, bisa gudunmawa da goyon baya da ya ba su, wanda ya taimaka wajen samun nasarorin hukumar.
Idris-Ahmad ya nuna godiyarsa ga gwamnatin Kano, hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya, da sauran masu ruwa da tsaki kan goyon bayan yakin da ake yi kan shan kwayoyi.
'Yan takara 20 na shan kwayoyi a Kano
A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar NDLEA reshen Kano ta ce an jirkita mata rahoton 'yan takarar zaben kananan hukumomin jihar na gwajin kwayoyi da ta yi masu.
Yayin da hukumar ta ce tabbas ta gano 'yan takara 20 masu tu'ammali da miyagun kwayoyi a Kano ta karyata rahoton da ke cewa 'yan takarar sun fito ne daga jam'iyyar NNPP.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng