Obasanjo Ya Tono Yadda Yar'adua Ya Hana Wata Alfarma da Ya Rokawa Dangote

Obasanjo Ya Tono Yadda Yar'adua Ya Hana Wata Alfarma da Ya Rokawa Dangote

  • Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana yadda marigayi Umar Musa Yar’adua ya ki amincewa da tayin Aliko Dangote na gudanar da matatun mai
  • Olusegun Obasanjo ya ce Dangote ya shirya tawaga kuma suka biya Dala miliyan 750 domin gudanar da matatun man Najeriya karkashin haɗin gwiwa
  • Yar’adua ya janye yarjejeniyar tare da maida wa Dangote kuɗinsa, wanda ya ce hakan ya janyo asarar fiye da Dala biliyan 2 ba tare da gyara matatun man ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT Abuja - Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana yadda gwamnatin sa ta yi ƙoƙarin gyara da gudanar da matatun man Najeriya tare da kamfanonin waje.

Obasanjo ya ce Alhaji Aliko Dangote ya same shi da wata tawaga domin tafiyar da matatun man Najeriya kuma sun kulla yarjejeniya.

Kara karanta wannan

Yadda dakarun Najeriya da Nijar suka cigaba da hada kai a faden daga

Obasanjo
Obasanjo ya fadi dalilin rashin farfado da matatun man Najeriya a baya. Hoto: Dangote Industries|Kola Sulaimon
Asali: Getty Images

A wata hira da gidan talabijin na Channels, Obasanjo ya ce gwamnatin Umar Musa Yar’adua ta dakatar da yarjejeniyar tare da maida wa Dangote kuɗinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sabanin Dangote da Yar'adua kan matatu

Tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ya ce ya nemi kamfanin Shell da su gudanar da matatun man Najeriya, amma kamfanin ya ƙi amincewa da tayin.

“Na tambayi Shell su ɗauki nauyin gudanar da matatun mu, amma sun ce ba za su iya ba saboda matsaloli da suka haɗa da ƙarancin albarkatun mai da cin hanci.”

- Olusegun Obasanjo

Obasanjo ya ce daga baya Dangote ya hada tawaga kuma suka biya Dala miliyan 750 domin gudanar da matatun mai ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da 'yan kasuwa.

Sai dai a cewar Obasanjo, bayan gama mulkinsa, Umaru Musa Yar’adua ya maidawa Dangote kudinsa tare da janye yarjejeniyar

Daily Trust ta wallafa cewa Obasanjo ya ce ya gana da Yar'adua domin bayyana masa muhimmancin yarjejeniyar, amma ya ce NNPCL zai iya gudanar da matatun.

Kara karanta wannan

"Tinubu na kan siraɗi": Peter Obi ya yi magana kan haɗa kai da Kwankwaso da Atiku

'Matatar Dangote za ta yi nasara' – Obasanjo

Olusegun Obasanjo ya ce yana da tabbacin matatar mai ta Alhaji Aliko Dangote za ta yi aiki sosai domin tana karkashin shugabanci mai zaman kansa.

A cewar Obasanjo, rashin amincewa da tayin Dangote ya janyo wa Najeriya asarar lokaci da kuɗi, amma matatar Dangote za ta zama mafita mai dorewa.

Kamfanin NNPCL ya farfado da matatar Warri

A wani rahoton, kun ji cewa kamfanin man Najeriya na NNPCL ya sanar da farfado da matatar mai ta Warri bayan shekaru.

Shugaban kamfanin, Mele Kyari ne ya bayyana haka a makon da ya wuce inda kuma ya fara shan yabo daga 'yan Najeriya ciki har da Bola Tinubu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng