Yadda aka 'Tsorata' Tinubu Ya Ki Karbar Minista a Gwamnatin Yar'adua
- Tsohon hadimin Muhammadu Buhari, Babafemi Ojudu ya bayyana yadda aka hana Bola Tinubu shiga gwamnatin marigayi Umaru Yar’Adua
- Babafem Ojudu ya ce mukamin minista zai iya zama barazana ga tafiyar siyasar Tinubu, wanda a lokacin shi ne jagoran jam’iyyar AC
- Ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola ya goyi bayan shawarar da aka bayar ta hana Tinubu karbar tayin Yar'adua
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tsohon hadimin shugaba Buhari, Babafemi Ojudu, ya bayyana yadda suka hana Bola Tinubu karɓar tayin zama minista a gwamnatin marigayi Umaru Musa Yar’Adua.
Rahotanni sun nuna cewa Babafemi Ojudu ya bayyana haka ne yayin wata hira da aka yi da shi a ranar Litinin.
Punch ta wallafa cewa Ojudu ya ce amincewa da mukamin zai iya tasiri a siyasar Tinubu, duba da abin da ya faru da wasu manyan shugabanni a baya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bola Tinubu ya ki zama ministan Yar'adua
Babafemi Ojudu ya bayyana cewa Tinubu ya kira shi wata rana tare da sanar masa cewa shugaba Yar’Adua ya masa tayin zama ministan kuɗi a gwamnatinsa.
Vanguard ta wallafa cewa Ojudu ya ce ya yi gaggawar gargadin Tinubu game da haɗarin da hakan zai iya haifarwa, lura da abinda ya faru da marigayi Bola Ige da aka kashe.
“Na ce masa, ‘Kana cikin AC. Shin ba ka karanta tarihin abin da ya faru da Bola Ige ba? Idan ka karɓi wannan mukami, kai ma kana iya shiga irin matsalar.’”
- Babafemi Ojudu
Aregbesola ya goyi bayan shawarar Ojudu
Babafemi Ojudu ya ce lokacin da ake tattaunawar, tsohon gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola, ya shigo wajen kuma ya goyi bayan shawarar da aka bayar.
“Femi yana da gaskiya. Wannan ba mukami ba ne da ya dace a karba.”
- Rauf Aregbesola
Ojudu ya ƙara da cewa wani ɗan kasuwa ya shiga cikin tattaunawar tare da bayyana cewa wannan tayin zai amfani kowa da kowa, amma shi da Aregbesola sun dage cewa ba haka ba ne.
Tinubu ya dawo da darasin tarihi a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta dawo da darasin Tarihi a makarantun Najeriya.
Rahotanni na nuni da cewa ministan ilimi ne ya bayyana dowowa da darasin bayan gwamnatin tsohon shugaban kasa Obasanjo ta soke shi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng