Yadda Dakarun Najeriya da Nijar Suka Cigaba da Hada Kai a Fagen Daga
- Rundunar tsaron Najeriya ta tabbatar da ci gaba da gudanar da hadin gwiwa da sojojin Nijar duk da ƙorafe-ƙorafen Janar Abdourahmane Tchiani
- Sojojin sun ce haɗin gwiwar na da nufin kawo ƙarshen ayyukan ta’addanci irin na Lakurawa da sauran kungiyoyin miyagu a iyakokin kasashen
- Rundunar tsaron ta bayyana cewa haɗin kai tsakanin ƙasashen biyu ne mafita ga matsalolin tsaro da suka addabi yankunan Najeriya da Nijar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Rundunar tsaron Najeriya ta sake tabbatar da kudurinta na ci gaba da gudanar da hadin gwiwa da sojojin Nijar duk da zarge-zargen da shugabannin sojin kasar.
Rahotanni sun nuna cewa wannan matakin yana daga cikin ƙoƙarin gwamnatin tarayya na kawo ƙarshen ‘yan ta’adda a iyakokin Najeriya da Nijar.
Majiyar Punch ta ruwaito cewa Manjo Janar Edward Buba ya bayyana cewa Najeriya ba za ta janye daga haɗin kai da sojojin Nijar ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dakarun Najeriya da Nijar suna aiki tare
Manjo Janar Edward Buba ya tabbatar da cewa sojojin Najeriya za su ci gaba da gudanar da aikin haɗin gwiwa da sojojin Nijar duk da rikicin siyasa da ke tsakanin shugabannin ƙasashen biyu.
"Sojoji za su ci gaba da gudanar da ayyukan sintiri da hadin gwiwa tare da sojojin Nijar."
- Manjo Janar Edward Buba
Tsohon jami'in da ya jagoranci hadakar tsaro tsakanin Najeriya da Nijar, CP Rabiu Ladodo (Mai ritaya), ya ce haɗin kai tsakanin ƙasashen ya ta'allaka ne da tsaron rayuka da walwalar al’umma.
Muhimmancin alakar kasar Najeriya da Nijar
CP Rabiu Ladodo ya bayyana cewa, shugabanni suna iya magana ta mahangar siyasa, amma idan ka kalli abin a hankalce, ba za a yi sakaci da tsaro da walwalar al’umma ba.
Ladodo ya ce dangantakar addini, al’adu da harshe suna tabbatar da haɗin kai tsakanin al’ummomin Jibia da Maradi duk da rikicin siyasa da aka samu a yanzu.
Ya ƙara da cewa haɗin kan sojojin biyu ya taka muhimmiyar rawa wajen magance ta’addanci, musamman na Boko Haram a Maiduguri da sauran iyakoki.
CP Ladodo ya ce haɗin kan sojojin Najeriya da Nijar yana taimakawa wajen yaki da ta’addanci da kuma rashin tsaro a yankunan Zamfara, Katsina da Sakoto.
Najeriya ta nemi zama da kasar Nijar
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta bukaci zaman sulhu da shugabannin Nijar kan tsaro.
Ministan harkokin wajen Najeriya ya bayyana cewa fahimtar juna zai kawo karshen zaman doya da manja da aka fara tsakanin kasashen biyu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng