Tsohon Jami'in Gwamnatin El Rufai Ya Shiga Hannun Jami'an Tsaro a Kaduna
- Rahotanni sun bayyana cewa jami'an tsaro sun cafke tsohon shugaban ma'aikatan fadar gwamnati a lokacin mulkin Nasir El-Rufai a Kaduna
- Jami'an tsaron na Operation Fushin Kada sun cafke Bashir Sa'idu ne a ranar Talata bisa zargin badaƙalar kuɗaɗe
- Sai dai majiyoyi na kusa da shi, sun nuna cewa kamun nasa na da alaƙa da siyasa domin ana farautar na kusa da tsohon gwamna El-Rufai
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Tsohon shugaban ma'aikatan fadar gwamnati a lokacin Nasir El-Rufai, ya shiga hannun jami'an tsaro.
Jami'an rundunar ƴan sanda na ‘Operation Fushin Kada’ wacce a baya aka fi sani da ‘Operation Yaki’ a jihar Kaduna ne suka cafke Bashir Saidu.
An cafke tsohon jami'in gwamnatin El-Rufai
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa rundunar ƴan sandan sun cafke Bashir Saidu, ne a ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Har yanzu dai ba a bayyana dalilin da ya sa aka kama shi ba, sai dai ana zargin ana tsare da shi ne bisa zargin badaƙalar kuɗaɗe, cewar rahoton jaridar The Cable.
Sai dai wasu majiyoyi na kusa da tsohon jami'in gwamnatin sun yi zargin cewa kamun da aka yi masa na da alaƙa da siyasa, domin hukumar na yin aiki ne bisa umarnin musgunawa mutanen El-Rufai a jihar.
An zargi gwamnati da farautar mutanen El-Rufai
Wani tsohon kwamishina a gwamnatin El-Rufai, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da kamun, yana mai cewa ya samu labarin an tsare Bashir Saidu a gidan yari na jihar.
"Gaskiya ne cewa jami'an tsaro sun kama shi a ranar Talata kuma yanzu haka yana gidan gyaran hali."
"Shin irin wannan dimokuradiyya ce suke son gudanarwa ta hanyar amfani da jami'an Operation Yaki wajen tsare abokan hamayyar siyasa?"
- Wata majiya
Ya kuma bayyana kamen a matsayin wanda akwai a siyasa a ciki, inda ya ce da yawa daga cikin waɗanda ake ganin na kusa da El-Rufai ne suna fuskantar tuhuma a kotun da’ar ma’aikata, EFCC ko ICPC.
El-Rufai ya taɓo batun ritaya a siyasa
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai, ya taɓo batun lokacin da za a daina jin ɗuriyarsa a cikin harkokin siyasa.
Malam Nasir El-Rufai ya bayyana cewa ko kaɗan babu batun yin ritaya daga al'amuran siyasa a gabansa, inda ya ce yana daram za a ci gaba da fafatawa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng