"Za a Ji Dadi," Majalisa Ta Fadi Yadda Amincewa da Kudirin Haraji zai Canja Najeriya

"Za a Ji Dadi," Majalisa Ta Fadi Yadda Amincewa da Kudirin Haraji zai Canja Najeriya

  • Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya bayyana cewa 'yan kasar nan za su samu jin dadin dimukuradiyya a kasar nan
  • Ya ce hakan zai tabbata da zarar Majalisar Dokokin kasar nan ta amince da kudirin harajin da gwamnatin tarayya ta gabatar
  • Sanata Godswill Akpabio ya kuma taya 'yan Najeriya murnar shiga sabuwar shekarar 2025, inda ya ce shekarar za ta zo da arziki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, a ranar Laraba ya sanar da ‘yan Najeriya lokacin da za su fara jin dadin ribar dimokuradiyya.

Ya bayyana cewa hakan zai faru ne idan Majalisar Dokoki ta amince da kudirin gyaran haraji kuma Shugaban Kasa Bola Tinubu ya rattaba hannu a kansa.

Kara karanta wannan

PDP, Obi sun ba Tinubu lakanin samo waraka daga matsalolin Najeriya

Godswill
Shugaban Majalisar Dattawa ya sake nanata muhimmancin kudurin haraji Hoto: Godswill Obot Akpabio
Asali: Facebook

Arise Tv ta ruwaito cewa Akpabio, wanda ya yi wannan tsokaci cikin wata sakon sabuwar shekara da ya sanya wa hannu da kansa a ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Kudirin haraji zai taimaki Najeriya” — Akpabio

Jaridar The Nation ta wallafa cewa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce Shugaban Bola Tinubu da gaske ya ke son ci gaban Najeriya.

Ya ce:

“Daga cikin gyare-gyaren da gwamnatin nan ta kaddamar, musamman kudirin gyaran haraji, ina tabbatar wa da ‘yan Najeriya cewa za mu fara jin dadin dimokuradiyya mai dorewa a wannan Sabuwar Shekara.”

“2025 za ta yi kyau” — Sanata Akpabio

Shugaban Majalisar Dattawa ya taya ‘yan Najeriya na gida da kasashen waje, murnar sabuwar shekara, inda ya ce al'amura za su daidaita a wannan lokacin.

Ya kara da cewa:

“Mu fara kallon sabuwar shekara ta 2025 da bege da fata mai kyau, kuma tare da hadin kai, za mu iya kai Najeriya ga babban matsayi.”

Kara karanta wannan

Awanni da sukar kudirin harajin Tinubu, Abba Gida Gida ya gana da shugaban kasa

Apkabio ya yi barazanar siyasa

A wani labarin, kun ji cewa shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya cika baki, inda ya bayyana cewa APC ta na da niyyar kwace wasu jihohi da 'yan adawa ke mulki.

Sanata Akpabio, wanda ya bayyana haka a lokacin da ya karbi baƙuncin Gwamna Monday Okpebolo a Uyo, ya ce sun shirya lashe zabuka a dukkanin jihohin Kudu maso Gabas.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.