Bello Turji Ya Fara Kai Hare Hare, Mahaifar Tsohon Gwamna na Tsaka Mai Wuya

Bello Turji Ya Fara Kai Hare Hare, Mahaifar Tsohon Gwamna na Tsaka Mai Wuya

  • Tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Attahiru Bafarawa ya tabbatar da Bello Turji ya fara kai hare-hare tun kafin wa'adin da ya bayar ya cika
  • Attahiru ya ce Turji da mayakansa sun kai farmaki wani kauye ranar Talata, kuma a halin yanzu ba a iya bin hanyar zuwa Bafarawa
  • Tun farko Bello Turji ya yi barazanar kai hare-hare kan jama'a idan jami'an tsaro suka ƙi sako abokinsa da suka kama a asibitin Shinkafi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sokoto - Gawurtaccen ɗan bindigar nan, Bello Turji, ya fara kai hare-hare a kauyukan da ke kusa da sansaninsa sa’o’i kadan kafin cikar wa’adin da ya bayar.

Tsohon gwamnan Sakkwato, Alhaji Attahiru Bafarawa ne ya bayyana hakan ga manema labarai, ya roƙi jami'an tsaro su kawo karshen ta'addancin ƴan fashi.

Attahiru Bafarawa.
Tsohon gwamnan Sakkwato ya tabbatar da cewa Bello Turji ya fara kai hare-hare Hoto: Attahiru Bafarawa
Asali: Twitter

Bello Turji ya yi barazanar kai hare-hare

Kara karanta wannan

"Tinubu na kan siraɗi": Peter Obi ya yi magana kan haɗa kai da Kwankwaso da Atiku

Idan ba ku manta ba a wani faifan bidiyo da ya saki, Bello Turji ya bukaci jami'an tsaro su sako na hannun damansa, Bako Wurgi da suka kama a asibitin Shinkafi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Leadership ta ruwaito cewa Turji ya yi barazanar kai hare-hare kauyukan da ke yankinsa a Zamfara da Sakkwato idan ba a biya masa buƙatarsa ba zuwa ƙarshen Disamba.

Amma da yake hira da ƴan jarida a gidansa da ke Sakkwato, Bafarawa ya ce Bello Turji ya fara kai hare-hare ƙauyuka tun kafin wa'adin da ya gindaya ya cika.

Turji: Akwai hadari a hanyar zuwa Bafarawa

“Wa’adin da Bello Turji ya bayar na neman a sako abokinsa da jami’an tsaro suka kama, abin damuwa ne matuka, kuma bai kamata a yi wasa da shi ba.
"Turji, wanda ya yi barazanar fara kai hare-hare daga ranar 1 ga watan Janairu, 2025 idan ba a yi abin da ya nema ba, ya riga ya fara kai farmaki kan jama'a.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi kofar rago ga Bello Turji, ana kokarin cafke shi

“Da misalin karfe 2:00 na tsakar rana a ranar Talata, 31 ga watan Disamba, 2024, na samu labarin harin da ya kai a wani kauye. Yanzu da nake magana babu tsaro a hanyar zuwa garinmu Bafarawa."

Bafarawa ya buƙaci a magance ƙalubalen tsaro

Da yake bayyana yadda lamarin tsaro ya taɓarɓare, Bafarawa ya ce dukkan mutanen kauyukan da ke kusa da garinsu Bello Turji sun bar gudajensu.

Tsohon gwamnan ya jaddada cewa matsalar ƴan bindiga ba karama ba ce kuma idan aka samu nasarar maganceta da sauran kalubalane tsaro, tattalin arziki zai bunkasa.

DHQ ta ce Turji ya kusa zama gawa

A wani rahoton, kun ji cewa babbar hedkwatar sojojin Najeriya ta bayyana cewa Bello Turji mataccen ɗan ta'adda ne da ke jiran lokacinsa.

DHQ ta bayyana cewa ta kashe manyan kasurguman ƴan ta'adda a faɗin ƙasar nan kuma sojoji na nan zuwa kan Bello Turji.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262