Tinubu Ya Kawar da Fargabar Gwamnoni kan Kananan Hukumomi, Ya ba Su Tabbaci
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya karɓi baƙuncin wasu daga cikin gwamnonin Najeriya a gidnasa da ke Legas
- Mai girma Bola Tinubu ya yaba da muhimmiyar rawar da gwamnonin suke takawa wajen ganin Najeriya ta ci gaba
- Tinubu ya kawar da batun saɓani tsakaninsa da gwamnonin kan yunƙurinsa na ba ƙananan hukumomi ƴancin cin gashin kansu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Legas - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa yana takun saƙa da gwamnonin jihohi kan ƴancin ƙananan hukumomi.
Shugaba Tinubu ya musanta raɗe-raɗin rashin jituwa tsakaninsa da gwamnonin kan yunƙurinsa na samar da ƴancin cin gashin kan ƙananan hukumomi a faɗin ƙasar nan.
Bola Tinubu ya karɓi baƙuncin gwamnoni
Hakan na ƙunshe a cikin jawabin da ya yi ga gwamnonin jihohin da suka kai masa ziyarar sabuwar shekara, wanda hadiminsa Dada Olusegun ya sanya a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnonin sun ziyarci Tinubu ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima a gidansa da ke Legas.
Shugaba Tinubu ya jaddada muhimmiyar rawar da gwamnonin jihohi ke takawa wajen ciyar da Najeriya gaba, inda ya ce shugabancinsu na da muhimmanci wajen samar da abinci, wadatar tattalin arziƙi da ci gaban ƙasa cikin sauri.
Me Tinubu ya ce kan ƴancin ƙananan hukumomi?
Da yake bayyana ƙudirinsa kan ƙananan hukumomi da cin gashin kansu, shugaban ƙasan ya jaddada muhimmancin hakan ga ci gaban ƙasa tare da kawar da jita-jitar rashin jituwa da gwamnoni.
"Ba za mu yi faɗa a tsakaninmu ba. Zan jagoranci canji. Ku yi iko a ƙananan hukumominku. Kuna iya maido da fatan jama'a ta hanyar samar da abin da mutane suke tsammani a matakin farko."
"Akwai jita-jita cewa mun samu saɓani kan cin gashin kan ƙananan hukumomi. A'a kawai a kawo cigaba a ƙananan hukumomi."
"Babu wanda yake so ya ƙwace su daga gare ku, amma muna buƙatar haɗin gwiwa. Mu yi aiki tare kuma mu tabbatar da cewa Najeriya ta amfana da hakan."
- Bola Tinubu
Gwamnatin Kano ta soki ƙudirin Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta yi adawa da ƙudirin harajin gwamnatin Bola Tinubu.
Gwamnatin ta Kano ta soki ƙudirin harajin wanda ke a gaban majalisa inda ta ce yana barazana ga haɗin kan ƙasar nan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng