'Yan Bindiga Sun Kai Harin Rashin Imani, Sun Kashe Karamar Yarinya da Wasu Bayin Allah

'Yan Bindiga Sun Kai Harin Rashin Imani, Sun Kashe Karamar Yarinya da Wasu Bayin Allah

  • Yan bindiga sun kai hari a kauyen Kuki a yankin ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna ranar Litini da tsakar rana
  • An ruwaito cewa maharan sun halaka wata yarinya ƴar kimanin shekara bakwai da wasu mutum biyu, sun sace shanu da kayayyaki
  • Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce ƴan banga daga Neja da Kaduna sun yi nasarar kwato shanun a wani daji

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna - Wasu miyagun ƴan bindiga sun kai farmaki kauyen Kuki da ke karkashin gundumar Randagi a ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

Maharan sun hallaka wata ƙaramar yarinya ƴar kimanin shekara bakwai da haihuwa da mummunan harin.

Malam Uba Sani.
Yan bindiga sun halaka ƙaramar yarinya da wasu mutum 2 a Kaduna Hoto: @ubasaniUS
Asali: Twitter

Majiyoyi daga yankin sun ce ‘yan bindigar a kan babura sun kai wannan harin rashin imani ne a ranar Litinin da misalin karfe 12 na rana, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Wani mutumi ya harbi abokinsa kan gardama a otal, yan sanda sun kai ɗauki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindiga sun kai hari a Kaduna

Kauyen Kuki dai na kan iyakar jihohin Neja da Kaduna kuma an ruwaito cewa ƴan bindigar sun sace shanu, sannan sun fasa shaguna sun ɗebi kayayyaki.

Wani shugaban al’umma da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce an tsinci gawar yarinyar ‘yar shekara bakwai a wani daji da ke kusa da kauyen bayan ‘yan fashin sun tafi.

Majiyar ta ce ‘yan bindigar sun biyo ta wani kauye da ake kira Unguwar Mission a lokacin da za su farmaki kauyen Kuke da tsakar rana.

Yadda suka kashe yarinya da wasu mutum 2

"Lamarin ya faru ne a tsakar ranar Litinin lokacin da ‘yan fashin suka shiga kauyen Kuki da ke karkashin gundumar Randagi.
"Sun saci shanu da babura, sun wawure shaguna kuma garin haka ne aka kashe mutane biyu, sannan mun gano gawar wata yarinya ‘yar shekara bakwai a wani daji da ke kusa,” in ji shi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bude wuta ana shirye shiryen jana'iza, an rasa rayuka

Ƴan banga sun kwato shanun da aka sace

Ya kara da cewa ‘yan banga daga Neja da kuma kauyen Randagi sun yi nasarar kwato shanun da aka sace a cikin dajin Uragi.

A cewar mutumin, ƴan bangan sun bi sawun maharan har cikin dajin bayan faruwar lamarin, suka masu kawanya.

Shugaban kungiyar zaman lafiya da ci gaba a yankunan da ke iyakokin Birnin Gwari da Neja (BG-NI CUPD), Ishaq Usman Kasai, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Gwamnatin jihar Kaduna da rundunar ‘yan sanda ba su fitar da wata sanarwa kan lamarin ba har kawo yanzu.

Yan bindiga sun kwace abincin kirismeti

A wani rahoton, an ji cewa miyagun ƴan bindiga sun kwace kayan abinci na kirismeti daga hannun wani mutumi a kauyen Gidan Abe da ke jihar Kaduna.

Wani shugaban al'umma ya ce mutumin ya gamu da wannan tsautsayi ne bayan ya sayo buhun shinkafa da wasu kayayyaki domin shirya zuwan kirismeti.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262