Gwamnatin Kano Ta Soki Kudirin Harajin Gwamnatin Tinubu, Ta ba da Shawara
- Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta yi fatali da ƙudirin haraji da ke gaban majalisa
- Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa ƙudirin bai dace ba a daidai lokacin da ƴan Najeriya ke fama matsalar tsadar rayuwa da talauci
- Gwamnan ya buƙaci shugaban ƙasa ya maida hankali wajen tsamo ƴan Najeriya musamman na yankin Arewaci daga cikin ƙangin talaucin da suke ciki
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta yi magana kan ƙudirin haraji na gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta yi magana da kakkausar murya dangane da ƙudirin harajin da ke gaban majalisar tarayya.
Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya bayyana matsayar gwamnatin ne ta bakin mataimakinsa, Aminu Abdussalam Gwarzo, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me gwamnatin Kano ta ce kan ƙudirin haraji?
Gwamna Abba ya bayyana hakan ne a yayin bikin murnar shigar 2025 da aka gudanar a filin wasa na Filin Mahaha, da ke Kofar Naisa.
"Wannan ƙudiri na sake fasalin haraji ba shine mafita ga ƙalubalen tattalin arziƙinmu ba. Jihar Kano ta tsaya tsayin daka wajen adawa da duk wani tsari da zai kawo illa ga rayuwar al’ummarmu."
"Wannan ƙudirin yanzu ba lokacinsa ba ne, ya fifita wasu sannan yana da illa ga haɗin kan ƙasa."
"Al’ummar Najeriya gaba ɗaya musamman a Arewacin ƙasar na ƙara fuskantar matsanancin hauhawar farashin kayayyaki da rashin tsaro da ba a taɓa ganin irinsa ba."
"Domin haka ya kamata fadar shugaban ƙasa ta ƙara maida hankali wajen magance matsanancin talauci da yunwa musamman a yankin Arewacin ƙasar nan."
- Abba Kabir Yusuf
Ɗan majalisar Kano ya soki ƙudirin haraji
A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗaya daga cikin ƴan majalisar tarayya daga jihar Kano, ya fito ya soki ƙudirin harajin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ɓullo da shi.
Dr. Mustapha Ghali ya bayyana cewa ko kaɗan ƙasar nan ba ta shirya aiwatar da sabon tsarin harajin da ake so ya fara aiki ba.
Ɗan majalisar ya nuna cewa aiwatar da sabon tsarin harajin zai kawo ɗimbin matsaloli ga ƙasar nan.
Asali: Legit.ng