Fitaccen Mawaki a Najeriya Ya Girgiza Intanet, Zai Auri Mata 3 a Rana Ɗaya a 2025

Fitaccen Mawaki a Najeriya Ya Girgiza Intanet, Zai Auri Mata 3 a Rana Ɗaya a 2025

  • Fitaccen mawaki a Najeriya, Dr. Arube Otor zai angonce da mata uku rana guda a watan Janairu, 2025 a jihar Delta
  • Ɗansa na riko ya bayyana cewa mawakin ya shirya auren mata huɗu ne rana ɗaya amma ɗaya ta janye saboda wasu dalilai na ƙashin kai
  • Mawakin ya taba auren mata biyu shekaru 20 da suka gabata amma ɗaya ta rabu da shi, yanzu mace ɗaya yake tare da ita

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Delta - Shahararren mawakin nan na Isoko highlife Dr. Arube Otor zai auri mata uku a rana guda a jihar Delta.

Wasu hotuna da ke yawo sun nuna Dr. Arube sanye da tufafin gargajiya tare da matan da zai aura, Oghenekome, Ewoma, da Oghenekaro, duk 'yan asalin jihar Delta.

Dr. Arube Otor da amarensa.
Mawakin Najeriya, Dr. Arube Otor zai auri mata uku rana guda Hoto: @Richyofficial1
Asali: Twitter

Ɗan riƙo na Arube kuma ɗaya daga cikin makusanta, Emperor Efih (Oscar), shi ne ya tabbatar da labarin auren, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Dan majalisar NNPP ya fallasa yadda ake lallashinsa don amincewa da kudirin haraji

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda mawakin ya shirya auren mata 4

A cewarsa, tun farko mawakin ya shirya angoncewa da mata huɗu amma ɗaya ta janye saboda wasu dalilai na ƙashin kai.

Ya ce duk da wannan tangarda da aka samu, za a ɗaura auren fitaccen mawakin da mata uku kamar yadda aka tsara a watan Janairu, 2025.

Dalilin mawakin na auren mata 3

Da yake bayyana dalilin da ya sa Arube ya yanke shawarar auren mata uku, Efih ya ce:

“Arube ya auri mata biyu kimanin shekaru 20 da suka wuce, ɗaya ta rabu da shi, ya koma zaman aure da mace ɗaya.
"Domin rage yawan kashe-kashen kudi, mawakin ya yanke shawarar auren mata hudu a wannan shekara, to kuma tun kafin a yi auren ɗaya ta janye."
"Fitaccen mawaki ne a jihar Delta, yana rera wakar addini, ya fara waƙa fiye da shekara 30 da suka wuce. Duk da haka a farkon rayuwarsa shi direba ne da ya haɗa waka da sana'a."

Kara karanta wannan

Rikicin sarauta ya ɗauki zafi, an kashe mutum 1 da faɗa ya kaure a wurin taro

Za a ɗaura auren ranar Lahadi 19 ga watan Junairu, 2025 a filin cocin Anglican da ke Landan Base yankin Uzere a karamar hukumar Isoko ta Kudu a jihar Delta.

Jarumar fim ta kirkiro manhajar haɗa aure

A wani labarin, kun ji cewa jarumar Nollywood, Chinonso Ukah ya bayyana shirinta na fara haɗa masoyan masu niyyar auren juna.

Jarumar ta kirkiro manhaja ta zamani da samari da ƴan mata za su rika haɗuwa, amma waɗanda suke da niyyar shiga daga ciki babu zancen yaudara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262