Muhimman Manufofi da Matakai 7 da Tinubu Ya Aiwatar a 2024
- Shugaban kasa, Bola Tinubu ya shafe kusan shekaru biyu kenan a kan madafun iko inda ya kawo wasu tsare-tsare
- Tinubu ya kawo sauye-sauye tun bayan hawansa wanda wasu daga cikinsu suka jawo maganganu daga yan kasar
- Sai dai shugaban ya tabbatar da cewa dukan matakan da ya ke dauka da tsare-tsare ya yi ne domin inganta Najeriya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - A shekarar 2024 da ta gabata, shugaban kasa, Bola Tinubu ya dauki wasu muhimman matakai domin kawo sauyi a kasa.
Tinubu ya kawo tsare-tsare da matakai ta kowane ɓangare a 2024 domin inganta rayuwar yan Najeriya.
Manyan matakai 6 da Tinubu ya dauka a 2024
Shugaban ya sanya hannu a wasu tsare-tsare da mafi yawan yan kasar ke ganin sun jefa ko za su jefa su cikin mummunan hali, cewar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit Hausa ta duba muku tsare-tsare da matakai da Tinubu ya tabbatar da su a 2024:
1. Kudirin ba dalibai tallafin karatu
Bola Tinubu ya rattaba hannu kan wannan kudiri inda ya zama doka a watan Afrilun 2024 da ta wuce.
An kirkiri wannan kudiri da aka sanyawa hannu ne domin tallafawa dalibai da ke manyan makarantu.
Tuni aka ƙaddamar da fara ba da tallafin ga dalibai da dama a manyan Jami'o'in kasar baki daya, cewar BusinessDay.
2. Sauya taken Najeriya
A ranar 29 ga watan Mayun 2024, Bola Tinubu ya sanya hannu kan dokar dawo da tsohon taken Najeriya da aka watsar a baya.
Tsohon taken Najeriya da aka dawo da shi 'Nigeria We Hail Thee' ya maye gurbin 'Arise O' Compatritots' da mafi yawan yan kasar suka saba da shi.
3. Mafi ƙarancin albashi
Shugaba Bola Tinubu ya amince da fara biyan mafi ƙarancin albashi daga N30,000 zuwa N70,000 saboda inganta rayuwar ma'aikata.
Tun bayan amincewa da sabon albashin, gwamnoni da dama suka sha alwashin biyan ma'aikatansu fiye da N70,000.
Jihohin Lagos da Rivers sun amince da biyan N85,000 ga ma'aikata yayin da wasu ke biyan sama da N70,000 a jihohinsu.
4. Karin albashin alkalai
A ranar 13 ga watan Agustan 2024, Bola Tinubu ya amince da kara albashi da alawus na manyan alkalai a Najeriya.
Tinubu ya ce ya dauki matakin ne domin rage yawan cin hanci da ake samu a bangaren shari'a.
5. Garambawul a mukaman Ministoci
A watan Oktoba 2024, Shugaba Tinubu ya yi gagarumin sauyin ministoci, inda ya nada sababbin ministoci bakwai, ya cire biyar, sannan ya sauya wa wasu goma ma’aikatu.
A cikin wannan sauyin, an sake sunan Ma’aikatar Raya Yankin Neja Delta zuwa Ma’aikatar ci gaban Yankuna, sannan an hade ma’aikatun yawon bude ido da al’adu.
6. Dokokin gyaran haraji
Gwamnatin Tarayya ta gabatar da kudirin gyaran haraji da ke nufin kawo sauyi kan yadda ake tattara harajin.
Wasu masana suka ce an yi hakan ne domin inganci, kara yawan haraji da bunkasa karfin tattalin arziki, da kuma saukaka wa talakawa nauyin haraji.
7. Yancin kananan hukumomi
A ranar 11 ga Yuli, 2024, Kotun Koli ta yanke hukunci mai muhimmanci da ya tabbatar da ikon kudin kananan hukumomi 774 na Najeriya.
Wannan mataki ya ba ƙananan hukumomi yancin samun kudinsu daga Gwamnatin Tarayya kai tsaye ba tare da katsalandan da gwamnoni ba.
Tinubu ya tura sako ga yan Najeriya
Kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ce shekarar 2025 za ta zo wa 'yan Najeriya da tulin arziki.
Tinubu ya ce gwamnati na sane da yadda jama'a su ka fada a cikin matsin rayuwa a watanni 19 da hawansa mulki.
Asali: Legit.ng