Gwamma Abba Kabir Ya Jero Ayyukan Ci Gaba da Zai Kawo Jihar Kano a 2025
- Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya aika sakon fatan alheri da murnar dhiga sabuwar shekarar 2025 ga Kanawa a faɗim duniya
- Gwamna Abba ya jinjinawa mutane Kano bisa jajircewar da suka yi a 2024 tare da fatan 2025 ta zo da alherai na samun sauƙin rayuwa
- Abba Kabir ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa za ta yi bakin ƙoƙarinta wajen yin ayyukan da za su amfani al'umma
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf ya miƙa sakon fatan alheri da murnar shiga sabuwar shekara ga mutanen Kano da ke ciki da wajen jihar.
Gwamna Abba ya bayyana yaƙini da fatan cewa shekarar 2025 ta zama mai cike da alheri da wadata.
Hakan na kunshe a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya wallafa a shafin Facebook ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Abba ya aika sakon sabuwar shekara
A cikin sakon nasa, gwamnan ya yaba da juriya da hakurin da mazauna Kano suka yi da matsin da aka shiga 2024, inda ya ba su tabbacin samun sauki a 2025.
"Ina yi wa Kanawa barka da shigowa sabuwar shekarar 2025, muna fatan wannan shekata ta kawo mana zaman lafiya, kwanciyar hankali da haɗin kai."
Gwamna Abba Kabir ya ce gwamnatinsa za ta yi ƙoƙarin ganin an amince da kasafin kudin 2025 a kan lokaci, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen kawo ci gaba a Kano.
Gwamnatin Kano ta shirya kawo ci gaba
A cewarsa, Kanawa za su ga ayyukan alheri a shekarar 2025 kama daga faɗaɗa harkokin kiwon lafiya, samar da ingantaccen ilimi da tallafawa manoma da kayan aiki.
Abba Kabir ya kuma bayyana aniyarsa ta kammala dukkan ayyukan da ya faro a kowane ɓangare domin su amfani al'umma.
Ya kuma bukaci mutanen Kano su kara haɗa kansu wuri guda kuma su marawa kudirorin gwamnatin baya domin cimma nasara a shirinsa na inganta rayuwarsu.
Gwamna Abba ya tuna da mata da matasa
Bugu da ƙari, Gwamna Abba ya jaddada shirin gwamnatinsa na tallafawa mata da matasa ta hanyar koyar da sana'o'i da faɗaɗa tsarin bayar da rance ga ƙananan ƴan kasuwa.
Ya ce yana fatan shekarar 2025 ta zo da alherai, sauƙin rayuwa da damarmakin bunkasa tattalin arziki a lungu da saƙon Kano.
Gwamnan Kano ya tsawaita wa'adin jami'ai
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Kano ya tsawaita wa'adin aikin shugaban ma'aikatan gwamnati jihar (HoS), manyan sakakarori da wasu manyan ma'aikata.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da kara masu shekaru biyu a bakin aiki wanda zai fara daga ranar 31 ga watan Disamba, 2024.
Asali: Legit.ng