2025: Farfado da Tattalin Arziki da Batutuwa 9 da Tinubu Ya Yi a Sakon Sabuwar Shekara

2025: Farfado da Tattalin Arziki da Batutuwa 9 da Tinubu Ya Yi a Sakon Sabuwar Shekara

Shugaba Bola Tinubu, a cikin saƙonsa na Sabuwar Shekara a ranar Laraba, ya jaddada kyakkyawar hasashen tattalin arziki na shekarar 2025.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos - Haka kuma shugaban ya kara da haskaka wasu daga cikin manyan nasarori da gwamnatinsa ta samu a shekarar 2024.

Tinubu
Tinubu ya yi alkawarin farfado da tattalin arziki Hoto: @officialABAT
Asali: Facebook

Mun tattaro maku batutwa 10 da aka gano a cikin furucin da shugaban Tinubu ya aika ga ‘yan Najeriya a sabuwar shekarar ta cikin sakon da Bayo Onanuga ya fitar.

1. Tinubu yi kyakkyawan hasashen tattalin arziki

Shugaba Tinubu ya jaddada kyakkyawan hasashen tattalin arziki na 2025, inda ya ce za samu nasarar ne saboda nasarorin da aka fara samu a 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cikin irin nasarorin 2024, The Nation ta ruwaito ya ce akwai farfadowar darajar Naira, samun riba a cinikayyar ƙasa da ƙasa na tsawon watanni tara a jere, da rage farashin man fetur.

Kara karanta wannan

"Wahalarku ba za ta tafi a banza ba," Tinubu ya aika sakon 2025 ga 'yan Najeriya

2. “An samu cigaban zuba hannun jari,” Tinubu

Shugaba Tinubu ya ce kasuwar hannun jari ta samu ci aba mai ban mamaki, wanda ya samar da riba na da biliyoyin Naira a shekarar da ta gabata.

Ya kara da cewa an samu karin zuba jari daga ƙasashen waje, wanda ya nuna cewa kasashen sun fara aminta da tattalin arzikin kasar.

3. Tinubu na shirin rage hauhawar farashi

Shugaban Najeriya ya bayyana cewa gwamnati za ta yi aiki don rage hauhawar farashi daga kashi wanda ya addabi ‘yan kasa a 2024.

Ya ce gwamnatin na da burin rage hauhawar farashin daga 34.6% zuwa 15%, ta hanyar ƙara samar da abinci da kuma inganta ƙera magunguna da kayan lafiya a cikin gida.

4. Tinubu: Za a kafa kamfanin ba da lamuni

A sabuwar shekarar da aka shiga, gwamnatin tarayya ta bayyana aniyarta na kafa kamfanin ba da lamuni na kasa kafin ƙarshen zangon biyu na 2025 saboda mutane da rukunoni marasa galihu, kamar mata da matasa, da kuma haɓaka tattalin arziki.

Kara karanta wannan

"Tinubu na da hali irin na Sardauna," Ganduje ya hango abin da zai faru a 2025

5. Tinubu zai gina tattalin arzikin $1trn

Gwamnatin tarayya ta ce babban burinta shi ne samun tattalin arziki mai darajar Dala tiriliyan ɗaya ta hanyar ci gaba da sauye-sauyen tattalin arziki da hadin kai tsakanin matakan gwamnati, ta hanyar mayar da hankali kan ci gaba.

6. Gwamnatin Tinubu za ta kaddamar da kundin kasa

Gwamnatin Tinubu ta bayyana aniyarta na ƙaddamar da kundin kasa da aka kira da ‘National Values Charter’ a farkon zangon shekarar 2025.

Shugaban kasa ya ce wannan zai inganta dabi’u masu kyau, ƙaunar ƙasa, da amana tsakanin ‘yan ƙasa da gwamnati.

7. Tinubu zai gudanar da taron matasa

A farkon shekarar 2025 ne gwamnati za ta kaddamar da taron matasa na kasa, don ƙarfafa matasan Najeriya su zama masu gina ƙasa, inda Ma’aikatar matasa za ta jagoranta.

8. “Za a hada kai tsakanin gwamnatoci,” Tinubu

An buƙaci gwamnatocin jihohi su haɗa kai da gwamnatin tarayya kan shirye-shiryen da suka haɗa da noma da kiwo.

Kara karanta wannan

"Carter mai son cigabanmu ne," Tinubu ya yi jimamin mutuwar tsohon shugaban Amurka

Tinubu ya kuma nemi a hada kai a kan sauye-sauyen haraji, tare da rungumar sauyin makamashi kamar CNG da motocin lantarki.

9. Tinubu ya nemi hadin kan jama’a

Shugaban kasa ya yi kira ga ‘yan ƙasa su kasance masu haɗin kai da tare da guje wa abubuwan da ke kawo rarrabuwar kawuna bisa siyasa, kabilanci, ko addini, domin samun nasarar shirin fatan sabuwar Najeriya.

10. Shugaba Tinubu ya godewa ‘yan kasa

Shugaba Tinubu ya nuna godiya ga sadaukarwar da ‘yan ƙasa suka yi a cikin watanni 19 da suka gabata, tare da tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa ƙoƙarinsu zai samar da ci gaba mai ɗorewa da kuma cimma burin ƙasa mai haske.

Bola Tinubu ya yabi 'yan Najeriya

A baya, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu gode wa 'yan Najeriya da yadda su ke hakuri da matsin da su ke ciki, musamman tun bayan hawansa mulki a 2023.

Kara karanta wannan

Tsohon hadimin Jonathan ya soki El Rufa'i kan zargin kabilanci a gwamnatin Tinubu

Ya ba wa 'yan kasar nan tabbacin cewa shekarar 2025 za ta bijiro da cigaban tattalin arziki da karuwar wadata a hannun 'yan Najeriya saboda manufofin da ake aiwatarwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.