Sojojin Najeriya, Amnesty Int'l Sun Fara Musayar Yawu kan Kisan Fararen Hula
- Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty Int'l ta zargi rundunar sojin Najeriya da kokarin rufe kisan jama'a a Sakkwato
- Shugaban kungiyar na Najeriya, Isa Sanusi ya ce yawan irin wadannan hare-hare sun sa dole a binciki ayyukan sojojin
- Amma a martanin rundunar, Daraktan labarai na rundunar tsaron kasar nan, Edward Buba, ya nemi bayanan Amnesty a rubuce
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Rundunar tsaron Najeriya da ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam, Amnesty Int'l, sun rika musayar yawu a kan jerin hare-haren bama-bamai da ake kai wa jama’a.
Yayin da ƙungiyar ta Amnesty ta dage cewa dole ne a binciki sojojin kuma a ɗauki mataki a kansu, sojojin sun zargi ƙungiyar da ƙin amsa gayyatarsu don tabbatar da zarge-zargenta.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Amnesty ta zargi sojojin da yunƙurin ɓoye kisan fararen hula a wasu al’ummomi mazauna Sakkwato.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amnesty Int'l ta soki sojojin Najeriya
Amnesty Int'l ta ce hare-haren sojojin Najeriya bisa kuskure ya jawo mutuwar fararen hula akalla 436 a cikin shekaru takwas da suka gabata.
Daraktan Amnesty Int'l a Najeriya, Isa Sanusi, ya bukaci sojoji su mika bayanai a kan harin sama zuwa ofishin Babban Lauyan Tarayya don gudanar da bincike.
Ya ce;
“Amnesty International na Allah wadai da abin da ke nuna yunƙurin sojojin Najeriya na ɓoye munanan hare-haren sama na ranar Kirsimeti da suka kashe aƙalla mutane 10 tare da jikkata wasu da dama a wasu al’ummomi biyu na ƙaramar hukumar Silame a Jihar Sokoto.”
Sojoji sun yi martani ga kungiyar Amnesty
Daraktan labarai na rundunar tsaron kasar nan, Edward Buba, ya ce sojojin za su amince da buƙatar Amnesty bayan ƙungiyar ta amsa gayyatar da aka yi mata.
Buba, wanda babban janar ne, ya ce;
“Mun gayyace su don mu tattauna kan wasu zarge-zargen da suka yi wa sojoji, waɗanda muka ga sun yi matuƙar tayar da hankali, suna ɓata suna, kuma abin takaici ne. Muna jiran su.
'Yan sanda sun yi martani ga Amnesty
A wani labarin, kun ji cewa rundunar 'yan sandan kasar nan ta caccaki rahoton da kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta fitar a kan kisan masu zanga-zanga.
Kungiyar ta zargi 'yan sanda da kashe mutane akalla 24 a lokacin zanga-zangar adawa da manufofin gwamnati, amma rundunar ta karyata rahoton tare da cewa ta yi aikinta.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng