An Dauko Wata Hanyar Warware Rikicin Kasar Nijar da Najeriya
- Gwamnatin Tarayya ta bayyana aniyarta na tattaunawa da gwamnatin Nijar domin rage zaman doya da manja a tsakanin kasashen biyu
- Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Yusuf Tuggar, ya yi kira da a gudanar da cikakkiyar tattaunawa kan matsalolin bisa ka’idodin ECOWAS
- Shugaban Sojin Nijar, Janar Abdourahman Tchiani, ya zargi Najeriya da yin aiki tare da Faransa domin kawo rashin tsaro a kasarsa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta bayyana aniyarta na tattaunawa da gwamnatin kasar Nijar domin warware rikicin diflomasiyyar da ke kunno kai tsakanin kasashen biyu.
Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Yusuf Tuggar, ya ce Najeriya na son ganin zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Yammacin Afirka ta hanyar amfani da tattaunawa da diflomasiyya.
Punch ta rahoto cewa Najeriya ta yi magana ne bayan korafin shugaban Nijar, kan zargin Najeriya da goyon bayan Faransa wajen kawo rashin kwanciyar hankali a kasarsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Najeriya ta nemi tattaunawa da Nijar
Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Yusuf Tuggar, ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya ta shirya gudanar da tattaunawa tsakaninta da Nijar bisa ka’idojin ECOWAS.
Yusuf Tuggar ya ce Najeriya tana mutunta ikon mallakar Nijar da iyakokinta tare da kira ga gwamnatin Nijar da ta shiga tattaunawar domin neman mafita.
Tuggar ya gargadi duk wani yunkuri na yada zarge-zargen da ba su da tushe, yana mai cewa hakan na iya haifar da rikice-rikicen da za su kawo cikas ga ci gaban yankin Afrika.
Tuggar ya ja hankalin duniya kan rikicin
Tuggar ya yi kira ga kasashen duniya da su tallafa wajen ganin an samu zaman lafiya a maimakon rura wutar rikici.
The Cable ta rahoto cewa ministan ya ce Najeriya ba za ta taba mara baya ga wani abu da zai kawo barazana ga tsaron Nijar ba.
Ya kuma jaddada cewa akwai bukatar girmama juna da hadin kai tsakanin kasashen biyu domin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.
Malami ya yi magana kan rikicin Nijar
A wani rahoton, kun ji cewa wani malamin addini a Najeriya ya yi magana kan yadda alakar Najeriya da Nijar ke neman dagulewa.
Sheikh Abubakar Malami ya nuna damuwa kan yadda wasu 'yan Nijar suke tsinewa Bola Tinubu akn zargin da shugabansu ya yi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng