"Wahalarku ba za Ta Tafi a Banza ba," Tinubu Ya Aika Sakon 2025 ga 'Yan Najeriya

"Wahalarku ba za Ta Tafi a Banza ba," Tinubu Ya Aika Sakon 2025 ga 'Yan Najeriya

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ce shekarar 2025 za ta zo wa 'yan Najeriya da kabakin arziki
  • Ya ce gwamnati na sane da yadda jama'a su ka fada a cikin matsin rayuwa a watanni 19 da hawansa mulki
  • Shugaba Tinubu ya shaida wa 'yan Najeriya cewa amincewa da suka yi ya jagorance su ya na karfafa masa gwiwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos - Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar wa 'yan Najeriya cewa dukkan sadaukarwar da suka yi cikin watanni 19 da ya karɓi mulki da watannin da ke tafe ba za su tafi a banza ba. A cikin sakon sabuwar shekararsa a safiyar Laraba, shugaban ya yi alkawarin ci gaba da yi wa al'umma hidima da tsakani da Allah.

Kara karanta wannan

Tinubu ya shiga jerin shugabannin duniya da suka yi fice a harkar rashawa

Tinubu
Shugaban kasa ya mika sakon sabuwar shekara ga 'yan Najeriya Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

A sakon da hadiminsa, Bayo Onanuga ya fitar a shafin Facebook, shugaban ya duk da kalubalen da gwamnatinsa ta fuskanta, an samu nasarorin da suka hada da raguwar farashin man fetur.

Bola Tinubu ya gode wa 'yan Najeriya

Jaridar Leadership ta wallafa cewa shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya godewa 'yan kasar nan da suka ba shi damar jagorantarsu a zaben 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Tinubu ya ce;

"Na gode da amincewarku da ku ka ba ni matsayin shugaban kasa. Amincewarku na ba Ni karfin gwiwa, kuma ina yi muku alkawarin ci gaba da yi muku hidima da gaskiya da zuciya daya."

"Za mu inganta rayuwarku a 2025," Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ta na aiki tukuru domin rage hauhawar farashi daga 34.6% zuwa 15%.

Ya ce;

"Farashin mai ya ragu a hankali, kuma mun samu ribar kasuwanci a na tsawon watanni uku a jere. Ajiyar kudin waje ya karu, kuma Naira ta karfafa kan Dala ta Amurka."

Kara karanta wannan

"Tinubu na da hali irin na Sardauna," Ganduje ya hango abin da zai faru a 2025

Tinubu ya yi alkawarin gwamnatinsa za ta gabatar da samun mafita daga kangin tattalin arziki da ya dabaibaye 'yan Najeriya tun bayan hawansa mulki.

Tinubu ya shiga jerin masu cin hanci

A wani labarin, kun ji cewa Cibiyar kula da manyan laifuka da cin hanci da rashawa ta duniya ta fitar da rahoto a kan shugabannin duniya da su ka shahara a rashawa.

An samu shugabannin kasashen Afrika biyu sun zo na biyu da na uku, yayin da hambararren shugaban Syria da ke neman mafaka a Rasha ya dauki kambun na daya a rashawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.