'Yan Sanda Sun Cafke Jami'in Tsaro Mai Taimakon 'Yan Ta'addan Boko Haram
- Rundunar ƴan sandan jihar Borno ta samu nasarar cafke wani jami'in tsaro na CJTF mai taimakon ƴan ta'addan Boko Haram
- Jami'in na CTJT wanda ake zargi da samar da kayan girki ga ƴan ta'addan ya shiga hannu ne bayan an samu bayanan sirri kan ayyukansa
- Kakakin rundunar ƴan sandan Borno ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba za a miƙa shi gaban kotu domin girbar abin da ya shuka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Rundunar ƴan sandan jihar Borno ta kama wani jami’in tsaro mai taimakon ƴan ta'addan Boko Haram.
Ƴan sandan sun cafke jami'in na rundunar CJTF, mai suna Muhammad Idrissa, bisa zarginsa da samar da kayan girki ga mayaƙan Boko Haram a jihar.
Jami’in tsaro ya shiga hannun ƴan sanda
Jami'in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar, Nahum Daso, ne ya bayyana hakan a ranar Talata, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kakakin ƴan sandan ya bayyana cewa, kama wanda ake zargin ya biyo bayan samun bayanan sirri ne game da ayyukansa.
Nahum Daso ya ƙara da cewa nan ba da jimawa ba za a gurfanar da Muhammad Idrissa a gaban kotu.
Meyasa yake taimakon ƴan Boko Haram
Da yake zantawa da manema labarai, Muhammad Idrissa ya amsa laifin da ake zarginsa da shi, inda ya ce yana taimakawa ƙaninsa ne wanda ɗan ƙungiyar Boko Haram ne.
"Kwanan nan na fara, kuma sau biyar kawai na kai musu. Na kan ba su kayan girki kamar su maggi, man girki, gishiri, da barkono."
"Ni mamba ne na rundunar haɗin gwiwa ta CJTF kafin a kama ni. Abin da nake yi shi ne, ina ba ƙanina kayan, ya kai su sansanin da yake zaune tare da ƴan uwansa ƴan Boko Haram."
"Ba ni da wani dalili na yin hakan. Ina taimakon ƙaramin ƙanina ne kawai, sanin cewa ba su da damar samun waɗannan abubuwan a inda suke."
- Muhammad Idrissa
Sojoji sun cafke ɗan Boko Haram
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'in rundunar sojojin Najeriya sun samu nasarar cafke wani ɗan ta'addan Boko Haram a jihar Taraba.
Rahotanni sun bayyana cewa wanda ake zargin yana fakewa ne da sayar da abinci wajen ba ƴan uwansa mafaƙa su aikata ta'addanci.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng