Duk da Barazanar Sojoji, Bello Turji Ya Ci Gaba da Ta'addanci a Zamfara

Duk da Barazanar Sojoji, Bello Turji Ya Ci Gaba da Ta'addanci a Zamfara

  • Bello Turji ya yi biris da roƙon da aka yi masa inda ya ci gaba da kai hare-hare kan bayin Allah a jihar Zamfara
  • Shugaban ƴan bindigan ya dawo kai hare-hare kan matafiya da da ƙauyukan da ke kan hanyar Shinkafi
  • Hare-haren na zuwa ne bayan wasu shugabannin Fulani sun zauna da Bello Turji domin ya janye barazanar da ya yi ta ci gaba da tayar da hankula

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Rahotanni sun bayyana cewa fitaccen shugaban ƴan bindiga, Bello Turji ya ci gaba da kai hare-hare a kan hanyar Shinkafi a jihar Zamfara.

Bello Turji ya bijirewa roƙon da manyan shugabannin Fulani suka yi a baya-bayan nan, kan ya yi watsi da barazanarsa.

Bello Turji ya kai hare hare a Zamfara
Bello Turji ya ci gaba da kai hari a Zamfara Hoto: @bulamabukarti
Asali: Twitter

Bello Turji ya ci gaba da kai hari a Zamfara

Kara karanta wannan

Yadda kauyuka 50 suka watse da Turji ya yi barazana, jigon APC ya shawarci Tinubu

Masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama ya bayyana hakan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyoyi sun bayyana cewa Bello Turji da mutanensa na kai hari kan matafiya da ƙauyukan da ke kan hanyar.

Hakan ya haifar da firgici da kuma hana zirga-zirgar jama'a a yankin.

Shugabannin Fulani sun zauna da Turji

Hare-haren na zuwa ne ƴan sa’o’i kaɗan bayan wasu manyan shugabannin Fulani na Shinkafi, Moriki, da Zurmi sun gana da Bello Turji.

A ganawar ta su sun buƙace shi da ya sake duba shirinsa na tayar da hankula tare da janye shingen da ya kafa a kan hanyar Shinkafi zuwa Gusau.

A yayin ganawar shugabannin sun yi kira da a kwantar da hankula tare da roƙon Bello Turji, ya yi watsi da shirinsa na sace-sace da kashe-kashen mutane musamman a Zamfara da jihar Sokoto.

Sai dai, Bello Turji bai bayar da wani tabbaci ba yayin ganawar, kuma bisa ga dukkan alamu bai ji roƙon da aka yi masa ba.

Kara karanta wannan

Tchiani: An samu bayanai daga kasar waje kan zargin Najeriya da hada kai da Faransa

DHQ ta faɗi makomar Bello Turji

A wani labarin kuma, kun ji cewa hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta bayyana cewa ƙarshen shugaban ƴan ta'adda, Bello Turji, ya kusa zuwa.

Daraktan yaɗa labarai na DHQ, Manjo Janar Edward Buba, ya bayyana cewa lokaci ya kusa cimma Bello Turji na tafiya zuwa inda ba a dawowa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng