Bayan Korar Sakatare da Kwamishinoni, Gwamnan Kano Ya Koma Kan HoS da Wasu Ma'aikata

Bayan Korar Sakatare da Kwamishinoni, Gwamnan Kano Ya Koma Kan HoS da Wasu Ma'aikata

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tsawaita wa'adin shugaban ma'aikatan gwamnatin Kano da wasu manyan sakatarori
  • Abba ya kara masu wa'adin shekaru biyu a bakin aiki kuma matakin zai fara ne daga ranar 31 ga watan Disamba, 2024
  • Haka nan kuma mai girma gwamna ya tsawaita wa'adin aikin wasu manyan ma'aikatan gwamnati da kwararru a fannin kiwon lafiya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya tsawaita wa'adin shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar da wasu manyan sakatarori da shekaru biyu.

Tsawauta wa'adin wanda zai fara daga ranar 31 ga watan Disamba, 2024 ya shafi wasu manyan ma'aikatan gwamnati a jihar Kano.

Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Gwamnan Kano ya karawa shugaban ma'aikata da wasu wa'adin shekara 2 a bakin aiki Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Tribune Nigeria ta tattaro cewa ƙarin shekarun aikin na kunshe ne a cikin wata dokar zartarwa da mai girma gwamna ya rattaɓawa hannu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daraktan yafa labarai na ofishin shugaban ma'aikata, Aliyu Yusuf shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Malamai da ma'aikata sun jefa gwamna a matsala kan sabon albashin N70,000

Matakin da gwamnan ya ɗauka ya yi daidai da tanadin sashe na 5 (2) da 208 na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya, 1999 da aka yi wa garambawul.

Waɗanda gwamna ya karawa shekarun aiki

Waɗanda matakin Gwamna Abba na tsawaita wa'adin aikinsu da shekara biyu ya shafa sun haɗa da Alhaji Abdullahi Musa, wanda zai ci gaba da zama shugaban ma'aikatan gwamnati (HoS).

Sai kuma manyan sakatarori da suka haɗa da Umar Muhammad Jalo, Bilkisu Shehu Maimota, Mu’azatu Isa Dutse, Abdulmuminu Musa, da Tijjani Muhammad Sharif.

Bugu da ƙari, dokar ta tsawaita wa'adin magatakardan majalisar dokokin jihar Kano, Bashir Idris Diso.

Gwamna ya tsawaita wa'adin malaman lafiya

Bayanai sun nuna cewa dukkan waɗannan ma'aikatan za su yi ritaya ne ranar 31 ga watan Disamba, 2024 amma a yanzu an ƙara masu shekara biyu a bakin aiki.

Har ila yau, Gwamna Abba ya kara wa’adin shekaru biyu ga wasu manyan ma’aikata da suka hada da Kabiru Ado Minjibir, Marwan Mustapha, Tajuddeen Bashir Baba, Hashim A. Sule, da Kabiru Inuwa.

Kara karanta wannan

Wani mutumi ya harbi abokinsa kan gardama a otal, yan sanda sun kai ɗauki

Sauran sun kunshi kwararru a fannin kiwon lafiya, Amina Idris, Ahmad Lawan, Hussaini Nuhu, Salisu H. Nadosun da Larai Ahmadu.

Kwankwaso ya yabawa Abba Kabir Yusuf

A wani rahoton, an ji cewa jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso ya ja hannkalin gwamnan Kano kan masu kokarin zuga shi ya tsaya da ƙafarsa.

Kwankwaso ya ce masu koƙarin ɗaba tsakaninsa da Gwamna Abba Kabir suna da wata manufa da suka ɓoye

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262