NLC Ta Gano Abin da Ya Kamata Gwamnati ta Maida Hankali a Kai a 2025
- Ƙungiyar ƙwadago ta fitar da saƙo yayin da ake shirin shiga sabuwar shekarar 2025 bayan zuwan ƙarshen 2024
- Shugaban ƙungiyar ya buƙaci gwamnatoci a dukkanin matakao su ba da fifiko kan walwala da jindaɗin ƴan Najeriya
- Ƙungiyar ta NLC ta kuma buƙaci gwamnatin tarayya da ta janye kuɗirin harajin da ta gabatar a gaban majalisa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta buƙaci gwamnatoci a dukkan matakai da su ba da fifiko kan walwala da jin dadin ƴan Najeriya a shekarar 2025.
Ƙungiyar ƙwadagon ta kuma buƙaci gwamnatin tarayya ta janye kuɗirin dokar harajin da ta gabatar a gaban majalisar tarayya.
Hakan na ƙunshe a cikin saƙon sabuwar shekara da shugaban ƙungiyar Joe Ajaero, ya fitar a shafin yanar gizo na NLC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wace shawara NLC ta ba gwamnati?
Joe Ajaero, ya ce ƙungiyoyin ƙwadago za su zage damtse wajen neman ƙarin albashin ma’aikata saboda rage tsadar rayuwa.
"Muna kira ga gwamnati a kowane mataki da ta tabbatar da cewa mulki ya zama abin da zai amfani jama'a. Jindadin ƴan kasa ya kasance shi ne dalilin farko na kasancewar kowace gwamnati."
"Samun abinci mai gina jiki, ingantacciyar kiwon lafiya, gidaje masu inganci, ilmi, sufuri da ƙarin tsaron rayuka da dukiyoyi gami da yancin shiga cikin yanke shawara kan yadda ake mulkarsu shi ne babban abin da mutane da ma'aikata ke fata."
"Domin haka dole ne manufofin gwamnati su nuna gaskiya, adalci, haɗa kai, rashin fifita wasu da rashin son zuciya."
"A kan haka ne muke sake kira ga gwamnatin tarayya da ta janye dokar harajin da ta ke gabatarwa a gaban majalisar tarayya domin dukkan masu ruwa da tsaki na ƙasa su kasance cikin tsarin."
Kungiyar NLC ta cacaaki gwamnatin Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta nuna takaicinta kan yadda takardun kuɗi suka yi ƙaranci a ƙasar nan.
Ƙungiyar ƙwadagon ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta nemo mafita kan matsalar ƙarancin kuɗin da ƴan Najeriya suka tsinci kansu a ciki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng