Tsohon Sanata Ya Yi Tonon Silili, Ya Fadi Hanyar Hana Yin Cushe a Kasafin Kudi

Tsohon Sanata Ya Yi Tonon Silili, Ya Fadi Hanyar Hana Yin Cushe a Kasafin Kudi

  • Tsohon sanata a majalisar dattawa ta tara, Shehu Sani ya gano bakin zarin kan cushen da ake yi a cikin kasafin kuɗi
  • Shehu Sani ya ce hanyar hana yin cushe ita ce samar da dokar da za ta hana ƴan majalisu sauya kasafin kuɗin ma'aikatu da hukumomi
  • Sai dai, ya nuna shakku kan cewa wannnan ƙudirin dokar da wuya ya tsallake karatun farko a majalisar tarayya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ɗan rajin kare haƙƙin jama’a kuma tsohon sanata, Shehu Sani, ya gano hanyar hana yin cushe a cikin kasafin kuɗi.

Shehu Sani ya bayyana hanyar da za a hana yin cushe ta hanyar ƙara abubuwa a kasafin kuɗin da ma'aikatu da hukumomin gwamnati suke gabatarwa.

Shehu Sani ya ba da shawara
Shehu Sani ya gano hanyar hana cushe a kasafin kudi Hoto: Shehu Sani
Asali: Facebook

Tsohon sanatan na Kaduna ta Tsakiya ya bayyana hakan ne a wnai rubutu da ya yi a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Duk da barazanar sojoji, Bello Turji ya ci gaba da ta'addanci a Zamfara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wace mafita Shehu Sani ya ba da?

Shehu Sani ya bayyana cewa hanyar hana yin cushen ita ce a samar da dokar da za ta hana ƴan majalisu, sauya kasafin kuɗin da hukumomi da ma'aikatun gwamnati suke gabatarwa.

Sai dai, ya nuna shakku kan cewa da wuya idan hakan zai yiwu, domin da ƙyar ƴan majalisun su yarda a yi dokar da za ta dakatar da yin hakan.

"Hanya ɗaya tilo da za a dakatar da cushe a kasafin kuɗi ita ce a samar da dokar da ta haramtawa ƴan majalisa yin katsalandan a kasafin kuɗin da ma'aikatu da hukumomin gwamnati suka gabatar.
"Amma ban san wanda zai kafa wannan doka ba ko kuma ta yaya za ta iya tsallake karatun farko."

- Shehu Sani

Shawarar tasa ta zo ne a daidai lokacin da ake shirin gudanar da taron kwamitin kasafin kuɗi tare da ministan kuɗi, ministan kasafin kuɗi da shugaban ofishin kasafin kuɗi na tarayya, a ranar Talata, 7 ga watan Janairu, 2025.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya fadi gaskiya kan cimma yarjejeniya tsakaninsa da Atiku, Peter Obi

Shehu Sani ya nemi a karrama sarakuna

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Shehu Sani ya buƙaci gwamnati ta karrama sarakuna da ƴan gwagwarmayar da suka yi wa turawan mulkin mallaka turjiya.

Tsohon sanatan na Kaduna ta Tsakiya wanda ya ziyarci inda aka birne wasu daga cikin sarakunan, ya bayyana cewa yana da kyau a tuna da sadaukarwar da suka yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng