Malamai da Ma'aikata Sun Jefa Gwamna a Matsala kan Sabon Albashin N70,000
- Malamai da ma'aikatan manyan makarantun Bauchi sun ayyana shiga yajin aiki kan rashin aiwatar da dokar sabon albashin N70,000
- Kwamitin haɗin guiwa watau JAC ne ya sanar da haka jim kaɗan bayan kammala taro ranar Litinin, 30 ga watan Disamba
- Shugaban kwamitin, Kwamared Abubakar Ahmed ya ce gwamnatin Bala Mohammed ba ta shirya biya masu buƙatunsu ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Bauchi - Malamai da ma'aikata na manyan makarantun gaba da sakandire da ke ƙarƙashin gwamnatin jihar Bauchi sun tsunduma yajin aikin sai baba ta gani.
Malamai da ma'aikatan sun fara wannan yajin aiki ne saboda gaza fara aiwatar da dokar sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000.
Kwamitin haɗin guiwa na malamai da ma'aikatan manyan makarantun Bauchi (JAC) ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa, kamar yadda Leadership ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ma'aikatan makarantu sun shiga yajin aiki
Shugaban JAC na jihar, Kwamared Abubakar Ahmed, ne ya karanta sanarwar a karshen taron gaggawa suka gudanar a sakatariyar ASUP a ranar Litinin.
Ya ce za su tsunduma yajin aikin gadan-gadan daga ranar Alhamis, 2 ga watan Janairu 2025.
Kwamared Abubakar ya ce matakin ya biyo bayan karewar yajin aikin gargadi na mako biyu da ma'aikatan suka yi daga ranar 16 zuwa 30 ga watan Disamba, 2024.
Ya ce babu wani mataki da ɓangaren gwamnati suka ɗauka na shawo kan ma'aikatan shiyasa suka yanke shiga yajin aikin sai baba-ta-gani.
Makarantun da ke ƙarƙashin kwamitin JAC
Kwamitin haɗin guiwa na JAC ya ƙunshi manyan makarantu biyar na gwamnatin Bauchi da suka haɗa da kwalejin fasaha ta Abubakar Tatari.
Sauran sun kunshi kwalejin ilimi ta Adamu Tafawa Balewa da ke Kagere, kwalejin ilimi da shari'a ta A.D Rufa'i, Musau da kwalejin Aminu Saleh da ke Azare.
Ragowar su ne kwalejin koyar da ilimin harkokin noma ta Bauchi da kuma kwalejin kiwon lafiya da fasaha ta Bill and Melinda Gates da ke Ningi.
Gwamnatin Bauchi ba da gaske take yi ba
Kwamitin hadin guiwa ya nuna rashin jin dadinsa da yadda wakilan gwamnatin jihar Bauchi ke bi wajen warware bukatunsu.
Injiniya Abubakar Ahmed ya kuma nuna damuwarsa kan yadda ake yin barazana da tsoratar da shugabannin JAC da mambobinsa a manyan makarantun jihar.
Gwamna Bala ya gana abokansa na firamare
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Bauchi, Sanata Bala Abdulƙadir Mohammed ya gana da ƴan ajinsu na firamare a wata liyafa da ya shirya.
Kauran Bauchi ya nuna farin ciki da jin daɗinsa bisa sake haɗuwa da abokansa waɗanda suka yi yarinta tare.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng