Gwamna Ya Cika Alkawari, Ya Faranta Ran Ma'aikata Ana Shirin Barin 2024
- Ma'aikatan jihar Oyo za su shiga cikin sabuwar shekarar 2025 cike da farin ciki bayan Seyi Makinde ya cika alƙawarin da ya ɗauka
- Gwamna Makinde ya biya ma'aikatan jihar albashin watan 13 wanda ya yi musu alƙawari a kwanakin baya
- Biyan albashin na zuwa ne makonni biyu bayan Gwamna Makinde ya amince a riƙa biyan N80,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Oyo - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya cika alƙawarin da ya ɗaukarwa ma'aikata na biyan albashin watan 13.
Gwamna Makinde ya sanya farin ciki a zukatan ma'aikatan jihar Oyo bayan an tura musu kuɗin a yammacin ranar Litinin, 30 ga watan Disamban 2024.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Prince Dotun Oyelade, ya fitar a ranar Talata, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Makinde ya biya ma'aikata albashi
Ya ce an biya kuɗin ne duk da yawan kuɗin da gwamnatin ke kashewa waɗanda suka kai N77bn duk shekara domin biyan albashin ma’aikatan jihar Oyo, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.
"Makonni biyu kacal da suka wuce, Gwamna Makinde ya amince da biyan N80,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatan gwamnati."
"Daga ranar 1 ga watan Janairu, 2025, za a riƙa kashe jimillar N143bn wajen biyan albashi duk shekara bisa amincewa da sabon mafi ƙarancin albashi. Wannan ya nuna ƙarin kaso 86% kan abin da ake biya a baya."
- Prince Dotun Oyelade
A cewarsa, hakan ya sanya jihar Oyo tana ɗaya daga cikin jihohi uku da suka fi biyan ma'aikata albashi mai tsoka a faɗin ƙasar nan.
Ya yi nuni da cewa jihar Oyo ce ke da yawan ma’aikatan gwamnati a yankin Kudu maso Yamma na Najeriya.
Gwamna Dauda ya amince a biya albashi
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince a biya ma'aikatan gwamnati albashin watan 13.
Shugaban ma'aikatan jihar ya bayyana cewa gwamnan ya amince a biya albashin ne domin ya zama alawus na shekarar 2024 ga ma'aikata.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng