Hajjin 2023: Gwamnati Ta Fara Biyan Alhazan Kaduna Kudin da Ta Yi Masu Alkawari
- Hukumar kula da alhazai ta jihar Kaduna ta sanar da fara biyan N61,080 ga Alhazai 6,239 da suka sauke farali a shekarar 2023
- Tun da fari, NAHCON ta bayyana cewa za a biya kudin ne sakamakon matsalar wutar lantarki da aka samu a dakunan alhazan
- Shugaban hukumar na Kaduna ya tabbatar da cewa alhazan za su karbi kudin kai tsaye cikin asusun banki bayan tantance su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - Hukumar kula da alhazan jihar Kaduna ta fara biyan N61,080 ga kowanne daga cikin alhazai 6,239 da suka yi aikin Hajji a 2023.
Wannan kudi sun fito ne daga hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) bayan an gano wasu matsaloli da suka faru lokacin aikin Hajjin 2023.
An fara biyan alhazan Kaduna N61,080
NAHCON ta ce an sami matsala a wajen samar da wutar lantarki yayin da alhazan ke zama a Muna, wanda ya shafi tsarin sanyaya dakunansu, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar alhazan Kaduna cikin sanarwa da kakinta, Yunusa Mohammed Abdullahi, ya fitar ta ce kowanne alhaji zai samu N61,080 saboda waccan matsalar.
Yunusa Abdullahi ya bayyana cewa hukumar za ta tura wadannan kudaden ne kai kai tsaye zuwa cikin asusun bankin alhazan da abin ya shafa.
An aika sako ga alhazan Kaduna na 2023
Sanarwar ta ruwaito shugaban hukumar, Malam Salihu S. Abubakar yana cewa:
“Za mu tabbatar da cewa alhazan da aka tantance bayanansu na asusun banki ne kawai za su karbi wannan kudi.”
Sanarwar ta kara da cewa alhazan da ba su mika bayanansu ba, su tuntuɓi jami’an rajista na kananan hukumomi domin gabatar da bayanai da tantancewa.
Malam Salihu S. Abubakar ya bukaci jami’an rajistar da su tabbatar da bin ka’idoji domin ganin cewa an yi gaskiya da kuma bin tsari wajen biyan kudin.
Alhazan Kaduna sun rasu a Makkah
A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu alhazan jihar Kaduna sun rasu a kasa mai tsarki yayin da suke gudanar da aikin Hajji na shekarar 2023.
Mutuwar Bashir Umar Sambo daga Kubau da Sulaiman Abubakar daga Igabi ya sa adadin alhazan Kaduna da suka rasu a Makkah ya karu zuwa hudu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng