'Tinubu Bai Dace da Najeriya ba': Hadimin Osinbajo Ya Fadi Mai Nagarta da Zai Kawo Sauyi
- Tsohon hadimin shugaban kasa, Babafemi Ojudu, ya ce Bola Tinubu bai dace ya jagorancin Najeriya a wannan lokaci ba
- Ojudu ya bayyana cewa Farfesa Yemi Osinbajo zai iya jagorantar Najeriya da basira da hangen nesa fiye da shugaba Tinubu
- Ya ce manufofin Tinubu ba su dace da Najeriya a wannan lokaci ba, yana mai nuna rashin gamsuwarsa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohon hadimin shugaban kasa, Sanata Babafemi Ojudu, ya yi magana kan salon mulkin shugaba Bola Tinubu.
Fitaccen dan siyasar, Femi Ojudu ya Tinubu ba shi ne mutumin da ya dace ya jagoranci Najeriya a wannan lokaci da ake ciki.
Hadimin Osinbajo ya soki mulkin Tinubu
Ojudu ya yi wannan furuci ne a yayin wata hira da jaridar The Sun ta bibiya a ranar Litinin 30 ga watan Disambar 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Dan siyasar wanda ya taba yin aiki tare da Osinbajo, ya ce mai gidansa zai iya yin jagoranci mai inganci fiye da Shugaba Tinubu.
“Na yi aiki da Tinubu, kuma ina ganin cewa falsafarsa ta ‘Emi Lokan’ ba ta dace da wannan lokaci ba.”
“Da Osinbajo ya samu dama, Najeriya za ta kai mataki mai girma, amma hakan bai faru ba."
- Babafemi Ojudu
Ojudu ya yabi kwarewar da hangen nesan Osinbajo
Ojudu ya ci gaba da cewa Osinbajo mutum ne mai hangen nesa kuma ya kamata ya jagoranci Najeriya, cewar Tribune.
"Ba za ka iya zama shugaban kasa kai kadai ba tare da wata kungiya mai tsari ba, dole dukkan shugabanni su yarda da manufofinka da hangen nesanka.”
- Babafemi Ojudu
Osinbajo ya ba yan Najeriya shawara
Kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya jaddada cewa shiga harkokin siyasa na samar da mafita fiye da zanga-zanga.
Osinbajo ya yi kira ga matasa da su shiga cikin harkokin siyasa domin kawo sauyi mai dorewa, musamman a kasashen da ke ci gaba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng