An Nemi Karrama Sarakunan Arewa da Suka Yaki Turawan Mulkin Mallaka
- Sanata Shehu Sani ya yi kira ga 'yan Najeriya da gwamnati su karrama jaruman da suka tsaya tsayin daka wajen kare kasar daga mulkin mallaka
- Shehu Sani ya kai ziyara makabartar wasu Sarakunan Arewa da aka tsige kuma suka mutu a Lokoja saboda kin amincewa da mulkin Turawan Ingila
- Rahotanni sun nuna cewa Sanatan ya ce irin wadannan jaruman suna bukatar yabo da tunawa da irin gudunmawar da suka bayar ga Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kogi - Sanata Shehu Sani ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da al’ummar kasar su karrama jaruman 'yancin kasa da suka sadaukar da rayukansu wajen kare al'umma daga mulkin mallaka.
Da yake zantawa da manema labarai yayin wata ziyara zuwa makabartar Sarakunan Arewa a Lokoja, ya bayyana muhimmancin tunawa sadaukarwar da suka yi.
Sanata Shehu Sani ya wallafa bidiyon yadda ya shiga makabartar da tare da wasu mutane a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ziyarar makabartar sarakunan da aka tsige
Sanata Shehu Sani ya kai ziyara zuwa makabartar da sarakunan Arewa guda shida suka mutu bayan Turawan mulkin mallaka sun tsige su saboda kin amincewa da dokokinsu.
Punch ta wallafa cewa Sanatan ya ce:
“Na ziyarci kabarin tsohon Sarkin Kano, Malam Aliyu Abdullahi (Mai Sango), wanda ya mutu a 1903. Ya tsaya tsayin daka wajen kare mutuncin kasarsa daga mulkin mallaka.”
Kiran Shehu Sani ga gwamnati da jama’a
Shehu Sani ya bukaci 'yan Najeriya da su koyi darasi daga irin jajircewar sarakunan da suka sadaukar da rayukansu domin kare martabar kasarsu.
“Dole mu karrama wadanda suka nuna sadaukarwa domin kare Najeriya.
Wadannan sarakunan ba al'ummarsu ce ta tsige su ba, turawan mulkin mallaka ne saboda sun ki yarda da mulkinsu.”
- Shehu Sani
Shugaban al’ummar Lokoja ya yabi Shehu Sani
Etsu na Lokoja, Emmanuel Akamisoko Dauda-Shelika ya yaba wa Sanata Shehu Sani bisa ziyarar, yana mai bayyana ta a matsayin wani abu mai muhimmanci ga tarihi.
Emmanuel Akamisoko Dauda-Shelika ya ce ziyarar Sanata Shehu Sani ta nuna muhimmancin tunawa da gudunmawar 'yan mazan jiyan.
Shehu Sani ya yi martani ga El-Rufa'i
A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Shehu Sani ya yi martani ga tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i.
Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa bai kamata Nasir El-Rufa'i ya nuna damuwa kan yadda Bola Tinubu ke nada mukaman gwamnati ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng