"Wuce Gona da Iri," Dattawan Arewa Sun Ce a Biya Diyyar Wadanda Sojoji Suka Hallaka a Sakkwato

"Wuce Gona da Iri," Dattawan Arewa Sun Ce a Biya Diyyar Wadanda Sojoji Suka Hallaka a Sakkwato

  • Kungiyar Arewa ta bayyana damuwa a kan yadda jami'an tsaro, musamman sojojin sama ke kai hare-hare kan fararen hula
  • Manyan yankin sun kuma yi tir da harin da sojoji suka kai a kauyen Silame da ke jihar Sakkwato, har mutum 10 su ka rasu
  • Jami'in hulda da jama'a na ACF reshen Kano, Bello Sani Galadanci ya kara da cewa dole a taka wa hare-haren birki a cikin sauri

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano - Kungiyar ACF ta yi Allah wadai da harin bama-baman sojoji da aka kai wa al’ummar Silame a Jihar Sakkwato.

Sakataren yada labaran kungiyar na kasa, Farfesa Tukur Muhammad-Baba ya ce wannan wani kuskure ne da ba za a lamunta ba.

Kara karanta wannan

"Za mu hargitsa APC," Jigo a Kano ya ce za su bijirewa shugabancin Ganduje

Sokoto
ACF ta yi tir da kisan mazauna Sakkwato Hoto: @jrnaib2
Asali: Twitter

Jaridar Punch ta wallafa cewa kungiyar na ganin sakacin hukumomin tsaro wajen kai hari kan fararen hula.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“A biya mutanen Sakkwato diyya,” ACF

A tattaunawarsa da Legit a Kano, kakakin ACF a jihar, Bello Sani Galadanci ya nemi sojojin su biya diyyar rayukan mutane.

Ya ce;

“Mu na kira lallai a biya diyya ga iyalan wadanda abin ya shafa. Irin wannan abu fa ya faru bara a Tudun Biri, ba su ji ba, ba su gani ba, suna taron mauludi aka hallaka su.”

ACF ta shawarci gwamnatin Bola Tinubu

Kungiyar ACF ta bukaci gwamnatin tarayya da lallai ta binciki dalilai, tare da kawo karshen kisan jama’a da sojojin ke yi.

Bello Sani Galadanci ya kara da cewa;

“Lokaci ya yi da ya kamata a tsaya a sa hankali a yi binciken, kan abin da ke janyo irin wadannan kura-kurai.
Yanzu ana kiyasin cewa a kananan shekara irin wannan kura-kurai da ake yi ana yaki da ‘yan ta’adda, an kashe mutane kusan 400.”

Kara karanta wannan

An tsinci gawarwaki bayan mummunan hatsarin mota, mutane 13 sun kone kurmus

Rashin tsaro ya na firgita kungiyar ACF

A baya, mun ruwaito cewa kungiyar Arewa ta ACF ta bayyana fargaba a kan yadda matsalar rashin tsaro ke kara kamari a shiyyar, yayin da 'yan ta'adda ke cin karensu ba babbaka.

Shugaban kwamitin amintattun kungiyar, Alhaji Bashir Muhammad Dalhatu da ya bayyana fargabar, ya kara da cewa matukar ba a dauki mataki ba, Arewa za ta fada babbar matsala.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.