"Jiki duk Yunwa," Tsohon Shugaban Majalisa Ya Fadi Illar Barin Arewa a Talauci

"Jiki duk Yunwa," Tsohon Shugaban Majalisa Ya Fadi Illar Barin Arewa a Talauci

  • Tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan ya tunatar da shugabanni cewa akwai yunwa a Najeriya
  • Ya bayyana haka ne a jihar, yayin raba tallafin hatsi da wasu kayan abinci ga talakawa a mazabarsa ta Yobe ta Arewa
  • Sanata Ahmad Lawan ya ce barin jama'a a cikin yunwa zai kara jefa su a mawuyacin hali na kunci da karuwar talauci

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Yobe - Tsohon Shugaban Majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya ce ’yan Najeriya suna fama da yunwa kuma suna cikin mawuyacin hali.

Sanata Ahmad Lawan ya bayyana haka ne a bayan kaddamar da rabon hatsi da kayan abinci ga mabukata a yankin mazabarsa ta Yobe Arewa a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Cire tallafi a Najeriya ya jawo wa gwamnati kabakin arziki daga bankin duniya

Ahmad Ibrahim Lawan
Tsohon shugaban majalisa ya nemi a kawo karshen yunwa Hoto: Ahmad Ibrahim Lawan
Asali: Facebook

Arise TV ta ruwaito cewa ya yi kira ga shugabannin siyasa da su nemo mafita mai dorewa kan matsalolin tattalin arziki da tsaro da kasar ke fuskanta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Ahmad Lawan ya raba kayan abinci

Jaridar Thisday ta ruwaito cewa gwamnati ta na bukatar tallafin masu ruwa da tsaki wajen rage matsanancin halin yunwa da fatara da ake ciki.

Ya ce wannan na daga cikin dalilan da ya sa gidauniyarsa ta tallafa wa kokarin gwamnatin Yobe don ba wa talakawa da mabukata sauƙi, musamman a lokaci.

Sanata ya shawarci shugabanni don rage yunwa

A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Ezrel Tabiowo, ya sanya wa hannu, Sanata Lawan ya ce tallafin abinci taimako ne na wani dan lokaci.

Ya ce wannan mataki da wasu daga cikin ‘yan kasar nan ke yi ba zai warware matsalar yunwa da kawo karshen kalubalen da talakawan Najeriya ke fuskantar.

Kara karanta wannan

Majalisa: 'Za a iya samu jinkirin amincewa da kasafin kudin 2025'

Ahmed Lawan ya kara da cewa:

“Dole ne waɗanda suke da hali su taimaka wa waɗanda ke cikin bukatar. Ba boyayyen abu ba ne cewa yawancin ’yan Najeriya suna cikin mawuyacin hali.

Sanata ya kai agaji a jihar Yobe

A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon shugaban majalisa, Sanata Ahmed Lawan ya kai gudunmawa domin tallafa wa wadanda ambaliyar ruwa ya rutsa da su a Yobe.

Tallafin da ya kai ya biyo bayan ambaliyar da ta daidaita mazauna jihar da yawa, inda Yobe ta zama daya daga cikin jihohin da aka samu mummunan ambaliya a damuwar bana.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.