'Yan Bindiga Sun Bude Wuta Ana Shirye Shiryen Jana'iza, An Rasa Rayuka

'Yan Bindiga Sun Bude Wuta Ana Shirye Shiryen Jana'iza, An Rasa Rayuka

  • Rikici tsakanin ‘yan daba da jami’an tsaro ya yi sanadin mutuwar mutum bakwai a karamar hukumar Ihiala ta jihar Anambra
  • Rahotanni sun nuna cewa wasu mahara sun kai hari wurin shirye-shiryen jana’iza, inda aka bude wuta ba kakkautawa
  • Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Anambra ya bayar da umarnin gaggawa domin kamo wadanda suka aikata ta’addancin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Anambra - A kalla mutum bakwai, ciki har da jami’an tsaro biyu da fararen hula biyu, sun rasa rayukansu a wani rikici tsakanin ‘yan daba da jami’an tsaro a Ihiala a jihar Anambra.

Wani ganau ya shaida cewa rikicin ya faru ne a lokacin da ake shirye-shiryen jana’izar wani mamaci a yankin.

Sanda
An kashe mutane 7 a Anambra. Hoto: Nigerian Police Force
Asali: Facebook

‘Yan sandan jihar sun tabbatar da faruwar lamarin a Facebook tare da alkawarin daukar matakan da suka dace domin kamo masu hannu a harin.

Kara karanta wannan

Yadda aka tattaro wasu barayi da 'yan bola jari masu sayen kayan sata

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Barkewar rikici yayin shirye-shiryen jana’iza

Punch ta rahoto cewa ‘yan daba sun kai farmaki wurin da ake shirye-shiryen jana’izar mamaci da aka tsara yi ranar 2 ga watan Janairu, 2025.

Wani ganau ya ce maharan sun kai hari tare da bude wuta, abin da ya jawo martani daga jami’an tsaro a yankin.

Martanin rundunar ‘yan sandan Anambra

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Anambra, SP Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da cewa mahara sun kai hari kan jami’an tsaro da fararen hula.

Kwamishinan ‘yan sanda, CP Nnaghe Itam, ya jagoranci ziyarar duba wurin da lamarin ya faru tare da bayar da umarnin kamo wadanda suka aikata laifin.

Kira domin kwantar da hankali a Anambra

Kwamishinan ‘yan sanda ya jajanta wa iyalan wadanda suka rasa rayukansu tare da tabbatar da cewa rundunar za ta yi bakin kokarinta wajen kamo masu hannu a lamarin.

Kara karanta wannan

Wani mutumi ya harbi abokinsa kan gardama a otal, yan sanda sun kai ɗauki

Ya kuma kara da cewa za a dauki matakan da suka dace domin tabbatar da tsaro a yankin Ihiala da kuma maida martani ga duk wani hari makamancin haka.

An kashe 'yan bindiga 40 a Katsina

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta bayyana manyan nasarorin da ta samu a shekarar 2024.

Kwamishinan 'yan sandan jihar ya bayyana cewa sun kashe 'yan bindiga masu garkuwa da mutane kimanin 40 a cikin shekara daya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng